Zannuwa TV Muna Maraba Da Zuwanka/ki Wannan Shafin Namu Mai Albarka.

An Bude Wannan Gidan Jaridar Ne Domin Wallafa Labarai Da Rahotanni Ingantattun Kuma Masu Kayatarwa Cikin Harshan Hausa Zalla, Manufarmu Inganta Ilmi Da Kasuwanci Domin Cigaban Al'umma.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya kai ziyara ga iyalan marigayiya Ummulkhairi, matashiyar da aka kona a yankin Maraban ...
28/06/2026

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya kai ziyara ga iyalan marigayiya Ummulkhairi, matashiyar da aka kona a yankin Maraban Jos a makon da ya gabata.
A yayin ziyarar, gwamnan ya jajanta wa iyalan mamaciyar tare da bayyana alhininsa kan wannan mummunan lamari da ya girgiza al'umma. Ya tabbatar musu cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika.
Gwamna Uba Sani ya kuma bayyana cewa jami'an tsaro sun k**a mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da adalci. Ya yi kira ga al'umma da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar doka a hannunsu, tare da bai wa hukumomin tsaro hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya.

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.Cikin alhini da jimami ne muke sanar da rasuwar Alhaji Lawan Sarkin Fulanin Kanwa. Al...
27/06/2026

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.
Cikin alhini da jimami ne muke sanar da rasuwar Alhaji Lawan Sarkin Fulanin Kanwa. Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi masa rasuwa.
Za a gudanar da jana'izarsa a yau da misalin karfe 8:00, a gidansa da ke Kanwa.
Muna roƙon Allah (SWT) Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata kabarinsa da rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya ba iyalansa, 'yan uwansa da daukacin al'umma haƙurin jure wannan babban rashi.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Ameen Ya Rabbal Alameen. 🤲🕊️

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya shiga cikin jerin ƴa...
26/06/2026

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya shiga cikin jerin ƴan takara uku na ƙarshe a rukunin ƙwararrun masu bunƙasa harkokin yaɗa labarai a lokutan rikici, a Gasar Masu Magana da Yawun Jama'a ta shekarar 2026.

An bayyana cewa ya kai wannan matsayi ne sak**akon gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta harkokin yaɗa labarai da sadarwa a Jihar Kano.

Ana shirya lambar yabon ta NS Awards ne tare da haɗin gwiwar NIPR da Spokespersons Digest, kuma za a gudanar da bikin miƙa kyautar a watan Agustan 2026 a Abuja.

A baya ma, Kwamared Waiya ya samu lambobin yabo daga ƙungiyoyi da cibiyoyin ƙwararru daban-daban saboda gudunmawar da yake bayarwa a fannin sadarwa da hulɗa da jama'a.

Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha H. Akpoti-Uduaghan, ta karɓi takardar shaidar tabbatar da ita a matsayin ƴar takarar Sa...
25/06/2026

Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha H. Akpoti-Uduaghan, ta karɓi takardar shaidar tabbatar da ita a matsayin ƴar takarar Sanata a ƙarƙashin jam'iyyar PDP domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Bayan karɓar takardar, ta gode wa shugabannin jam'iyyar da magoya bayanta bisa amincewar da s**a nuna mata, tare da jaddada aniyarta ta ci gaba da wakiltar al'ummar Kogi ta Tsakiya da kuma kare muradunsu a majalisar dattawa.





Sama da mutum hamsin ne s**a mutu sak**akon ruwan bama-bamai da jiragen yaƙin Najeriya s**a yi wa wasu bayin Allah masu ...
12/04/2026

Sama da mutum hamsin ne s**a mutu sak**akon ruwan bama-bamai da jiragen yaƙin Najeriya s**a yi wa wasu bayin Allah masu cin kasuwar ƙauye a jihar Yobe, sai dai rundunar sojin ta ce hakan ya faru ne kan kuskure.

Rahotanni sun ce gomman mutane ne s**a jikkata a harin wanda a halin yanzu suke asibiti ana ba su taimakon gaggawa.

Kusan wannan shi ne karo na goma da rundunar sojin ke ruwan bamabamai kan waɗanda ba su ji ba su gani ba, sai daga baya a ce kuskure ne, kuma kullum a kan ƴan Arewa musulmai ake samun wannan kuskuren k**ar na Tudun Biri a Jahar Kaduna.

Muna addu'ar Allah yaji kansu da rahama.

Allah Ya Yiwa Alaramma Malam Ibrahim Dan Jariri Rasuwa A Daran Jiya. Tuni Aka Yi Jana'izarsa Yau Litinin Karfe 9:30 Nasa...
30/03/2026

Allah Ya Yiwa Alaramma Malam Ibrahim Dan Jariri Rasuwa A Daran Jiya.

Tuni Aka Yi Jana'izarsa Yau Litinin Karfe 9:30 Nasafe 30 - 3 - 2026 Zuwa Makabartar Kofar Mazugal.

Malam Ya Rayu Cikin Karantar Da Alqur'ani Da Hidima Ga Sharifai.

Allah Ya Jikansa Da Rahma.

Hotunan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero A Wajen Sallar Idin Ƙaramar Sallar Bana.
20/03/2026

Hotunan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero A Wajen Sallar Idin Ƙaramar Sallar Bana.

DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin jihar Kano ta rantsar da sabbin mambobinta biyuShugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ji...
03/03/2026

DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin jihar Kano ta rantsar da sabbin mambobinta biyu

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Isma’il Falgore, ya jagoranci rantsar da sabbin ’yan majalisa biyu a ranar Talata.

Sabbin mambobin su ne Sa’adu Aminu Sa’adu mai wakiltar Ungogo da Nabil Aliyu Sarki Daneji mai wakiltar Kano Municipal, wadanda s**a yi nasara a zabukan cike gurbi da Hukumar ta gudanar.

Dukkansu sun yi nasara a karkashin jam’iyyar APC, inda s**a maye gurbin iyayensu da s**a rasu a watan Disambar bara.

Yanzu Haka Wata Babbar Mota Ta Buge Wani Dan Sanda A Gaban Kurna Babban Layi Daidai Division Din Dragon Dake Kurna Kafin...
21/02/2026

Yanzu Haka Wata Babbar Mota Ta Buge Wani Dan Sanda A Gaban Kurna Babban Layi Daidai Division Din Dragon Dake Kurna Kafin Aje Gidan Man Aliko.

Dan Sandan Yana Tafiya A Mashin Kirar Jincheng.
Motar Tabi Takansa Ko Motsaya Baiyi Ba.

Yanzu Haka Gawarsa Tana Division Din Na Dragon.
Mai Motar Ya Kawo Kansa Bayan Ya Faka Motar.

Adresse

Democratic Republic Of The

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Zannuwa TV publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Raccourcis

Partager