09/09/2022
🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 69/70
___________Ahankali nanny ta fara magana ,tana cewa"Ammi ba ita bace asalin mahaifiyar Adeeb,amma itace wacce ta rikeshi bayan ta kashe mahaifiyarsa."
Dararrararaammm!!!gaban fattu ya bada ƙara, sak**akon jin maganar nanny datayi k**ar saukar aradu,
Da sauri ta dafe gefen kujerar da take kai,dan ji tayi k**ar zata faɗi.
Baki buɗe take kallon nanny cike da tsantsar mamaki,cikin rawar murya tace "nanny kina nufin ammi itace ta kashewa Hamma mahaifiyarsa?to amma me yasa Hamma yake mata kallon uwa?me yasa bai dauki mataki akanta ba?"fattu ta faɗa cikin rudani.
Ajiyar zuciya nanny tayi kafin tace "saboda bashi da masaniya akan abinda ya faru,kuma ya yarda da ammi fiye da kowa,dan yana mata kallon uwa mahaifiyane,baya tunanin zata taba cutar dashi.ki saurare Ni da kunnen basira ,zaki ji abinda ya faru yanzun nan.
"Sarauniya Nazli,ƴace agurin ƙarin baban mai martaba uwa daya uba daya,wato kenan ita da mai martaba ,yan uwan juna ne ,dan kuwa auren zumunci akayi musu.
Suna kaunar juna matuka bayan anyi auren,suna zamansu lafiya cikin so da aminci, lokacin da akayi auren nasu,iyayen sarauniya Nazli duk sun rasu,hakan yasa take zaune a hannun mahaifiyar mai martaba ,dalilin hankali da nutsuwarta yasa mahaifiyar mai martaba ta zaba masa ita matsayin matar da zai aura inda ranar da aka daura musu aure aka naɗa shi matsayin sarkin misra.
Shekara guda dayin aurensu Allah ya azurtata da zamu yaro , kyakykyawa abin so ga kowa, ranar suna aka rada masa suna adeeb.
Adeeb ya taso cikin so da kauna, agurin iyayensa, da ma duk wani wanda yake fadar nan,yana da matukar hakuri ,hazaka ,ladabi da kuma biyayya.
Nice wacce ke rainon Adeeb ,kasancewar mijina yana aiki acikin fadar nan,shine drivern dake tuka sarki da iyalinsa.
Lokacin ina goyon dana tareeƙ ,dan haka na hadasu duka ina rainonsu,saidai ko da wasa ban taba hada tareeƙ da Adeeb matsayi daya ba,duk l