09/10/2023
Shi adalci agun masu mulki wajibi ne. Hakanan duk wanda aka bashi wata amana ko shugabanci, to wajibi ne ya zama mai adalci da gaskiya wajen kiyaye amanar da aka bashi.
Idan mai mulki ya zamto adali to saboda albarkar adalcinsa Allah yakan kiyaye garinsa ko jiharsa ko ƙasarsa daga wasu bala'o'i da chututtuka da yawa. Kuma Allah yakan sanya albarka acikin jama'ar da yake jagoranta. Kasuwancinsu da nomansu da sana'o'insu duk zasuyi albarka.
Idan aka samu albarka acikin waɗannan abubuwan da na lissafa to in sha Allahu tarbiyyar al'ummar zata gyaru, yanayin zamantakewar aure za'a samu sauyi, ilimi zai bunkasa, zaman lafiya zai wanzu, kuma tattalin arzikin al'ummar zai bunƙasa.
Mu dubi irin ɗaukakar da daular musulunci ta samu a zamanin Khalifancin Sarkin Muminai Umar bn Khattab (Allah ya yarda dashi) wanda a lokacin sa sai da musulunci ya mamaye dukkan yankunan larabawa har da yankunan sauran ƙabilun nahiyar Asia, kai har daular turawan rum (Roman Empire) hantarsu takan kaɗa da zarar an ambaci sunan "UMAR" ko "ISLAM".
Saboda irin waɗannan nasarorin ne bayahuden Amurkan nan mai suna Micheal Hart bisa nazarinsa ya sanya sunan Sayyiduna Umar akan gaba-gaba acikin jerin manyan shugabannin da rayuwarsu tayi babban tasiri aduniya baki ɗaya.
A zamanin Sayyiduna Umar saboda tsantsar adalcinsa arziki ya mamaye ko ina acikin daula, har albashi yake biyan sauran sahabbai musamman Ahlu Badrin da Muhajirai, sannan gwamnatin musulunci a lokacin sa tana taimaka wa marayu da zaurawa da marassa galiho.
Adalcin Sayyiduna Umar (rta) yakai har watarana ya bugi wani daga cikin gwamnoninsa saboda laifin danne hakkin wani Kirista talakansa. Kunga tsantsar adalci kenan babu wariya, babu zalunci.
Saboda tsantsar adalcin da ya watsu a daularsa, sai gashi arziki ya yawaita a hannun jama'a, Kuma ayyukan laifi sun ƙaranta. Sai ayi shekara da shekaru ba'a samu wani yayi zina ko sata ba.
Ko a wannan zamanin namu, rashin adalcin da Shugabanninmu ke yi shine babban tushen lalata tarbiyyar al'ummah.
Yayin da Shugabanni basu damu da tsaron lafiyar kowa ba sai tasu, basu damu da kiwon lafiyan kowa ba sai nasu da iyalansu, basu damu da jin dadin kowa ba sai nasu, za'a take dokokin Allah basu damu ba, to ku saurari watsuwar bala'in cututtuka da kashe kashen rayuka da manyan laifuka a cikin al'umma.
Ya Allah ka gyara halayen Shugabanninmu, ka haɗa su da mashawarta na kirki, ka kyautata tattalin arzikinmu, ka yaye matsalolinmu, Muna kamun Qafa da soyayyar Annabinka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
(NYDAF-TEAM)
09/October/23.