15/11/2023
Da farko inaso na taya dukkan wani ko wata daya cika wannan skills programme na NITDA 3MTT murna na kasancewar daya daka cikin mutane masu nasara a wannan zamani duba da irin tarin alkhairan da zai biyo bayan wannan programme din
Jiya ina bincike akan tsarin NITDA 3MTT sai nake ganin sanarwa daka Minister of communication cewa daya daka cikin amfanin wannan skills din shine saboda matasa su samu aikin yi wajen dogaro da kansu sannan su samu tallafi a waje gwamnati
Gwamnatin Nigeria karkashin Minister of communication tare da hadin kan UNDP tace zata dauki matasa mutum dubu uku 3,000 aiki na internship wanda s**a fi kwarewa akan fannonin su sannan za'a dinga biyan su albashi duk wata
Wannan dama ce wanda kowa zai iya samun ta inhar mutum yayi abinda ya dace wajen bada hankalin shi akan wannan programme din ba sai kai dan wani bane ko ke yar wata ce a Nigeria ba wannan dama ce ga kowa
Ina mai tabbatar muku nan gaba duk wanda yayi wannan programme din sai yayi farin ciki da godiya ga Allah saboda irin alkhairan da zasu biyo cikin shi, akwai yiyuwar bayan an fara wannan program din NGO's zasu shigo ciki su tallafa wa matasa da kudi, Computers da sauran kayan na'ura na zamani
Ina tunanin zamu bude WhatsApp group wanda zamu dinga amfani dashi wajen ilimantar da juna da video's, shawarwari da bayanai masu amfani wanda zasu taimake mu akan wannan tsari saboda wasu inhar ba'a dinga taimaka musu zasu iya asaran wannan dama a gare su
Allah ya bamu nasara.
For More Information
09067179166
07010567325
Abubakar Sarkin Kira Gwaram