
06/05/2025
~TA’AZIYYA ZUWA GA AL’UMMAR KASAR DUGURI/GWANA..😭
~A madadin shi Kansa, ‘Yan uwa da iyalan sa, Mai girma Ambassador Air Marshal Sadiq Baba Abubakar (rtd), Yana mika sakon Ta’aziyyar sa zuwa ga iyalai, ‘Yan uwa, Masarautar Kasar Duguri da Masarautar Alkaleri, da sauran Al’umma baki daya bisa asaran Rayukan wasu Jaruman ‘Yan banga da s**a sadaukar da rayuwar su wurin Kare iyaye, iyalai da Yan uwan su a wannan Kasa ta Duguri/Gwana a jiya bayan sunyi arangama da wasu ‘Yan Ta’adda masu sace Dabbobi da sauran Dukiyoyin al’umma a Daji.
~Muna masu Addu’a da Fatan Ubangiji Allah ya musu Gafara da Rahamah, Yasa Mutuwa hutu ne a garesu baki daya, Ya Kuma dawo da zaman Lafiya da Lumana a wannan yanki da ma jihar Bauchi baki daya.
{Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum}