02/01/2025
Kwana biyu da s**a wuce, Professor Isa Ali Ibrahim Pantami, CON, (Majidadin Daular Usmaniyya) ya samu halartan taron wadanda s**a yi karatu a shekara daya a Government Science Secondary School Gombe, wanda sun Kammala karatu sama da shekara 31 da s**a wuce.
A wurin meeting din an yi jawabai daban daban na ci gaba da tsara ayyuka don ci gaban makarantar da jama'ah.
Principal na Government Science Secondary School ya yi bayani na musamman wajen fadan manya manya ayyuka da Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya kawo makarantar. Wasu daga cikin ayyukan sune:
1) Digital Capacity Building Centre of Government Science Secondary School Gombe.
2) yin gini na musamman na Emerging Technology Centre wanda aka sanya computoti na zamani sama da guda dari (100) da kuma wasu na'urori na musamman na Digital Economy.
3) Promotion of Digital Literacy by providing Laptops to some Teachers of Government Science Secondary School Gombe.
4) Sanya Solar Power a Computer Centre da kuma Generator na zamani.
5) Samar da modern borehole ta hanyar Corporate Social Responsibilities.
6) Samar da Laboratory na musamman akan Digital technology da karin computoti 20 da printer.
7) Hukumar makarantar ta bukaci ya Gina musu sabon Masallaci. Allah Ya bada ikon ya gina musu babban masallaci a cikin makarantar a matsayin sadaqa wa iyayensa (Allah Ya jikansu, Ya jikan namu iyayen)
A wurin taro, Principal na makarantar ya bayyana irin wadannan ayyuka da Professor Isa Ali Pantami ya yi a makarantar domin wakiltan abokanen karatun sa da s**a Kammala sama da shekara 31 da s**a wuce. Principal din ya kara yabo akan irin fice da nasarori da Professor Isa Pantami yasamu a rayuwa, sannan wannan makaranta tana alfahari da hakan.
Mataimakin shugaban dalibai na shekarar da s**a kammala wato Mr Ibrahim Umar Yila wanda ya jagoranci zaman, shi ma ya kara da godiya ga Professor Isa Ali Ibrahim Pantami akan jawaban Principal. Kuma ya kara da yabo akan ayyuka da Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya samawa wasu daga cikin abokan karatunsa a wannan makaranta da sauran makarantu, a Nigeria. Wasu har sun samu matsayi na CEO a gwannatin tarayya dalilinsa, wasu kuma sun samu har fita kasashen turai aiki dalilin taimakonsa.
Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi godiya ga abokan karatunsa, da kuma Award da s**a ba shi lokuta da dama, har da Award na shekara da ta gabata wanda Malam Yusuf Saleh Kilawa ya gabatar masa. Malam Yusuf Saleh Kilawa ya kara da bayyana cewa Professor Isa Ali Ibrahim Pantami, yana gayyatarsu gidansa daga lokaci zuwa lokaci su gana kan muhimman ayyuka, sannan kuma a Ramadhan yakan bukaci ni na gayyaci abokanen karatunmu wadanda suke rayuwa a Abuja don su gana da shi a gidansa, su kuma yi buda baki tare.
Wadanda s**a bayyana ayyukan alheri na Professor Isa Ali Ibrahim a wurin taron suna da yawa. Daga cikin su akwai Professor Dahiru Inuwa Ibrahim, da Malam Abdullateef Ibrahim, da Enginneer Muhammad Garba, da Malam Muhammad Danladi, da sauransu.
An kammala zama lafiya tare da addu'ar Allah Ya bamu tsawon kwana domin halattar tarurruka masu zuwa nan gaba in Allah Ya yarda.
Daga
Muhammad Yahaya Tambura
(2/01/2025).