12/05/2019
LADA DA SAKAMAKON YIN SALATI GA ANNABI ﷺ
Yin salati ga Annabi ﷺ wajibine akan dukkan musulmai baki daya,Kuma hakkin Annabi ﷺ akan dukkan al'umarsa suyi masa salati,musammama idan an ambaci sunansa,da ranar juma'a da daren juma'a,da bayan kiran sallah,da dukkan lokacin da kasami lokaci.
Yin salati ga Annabi ﷺ yana da falala da lada mai yawa,babban ladarsa shine,samun ceton Annabi ﷺ da samun kasanci da shi a ranar alqiyama da kuma sanin sunka a wajansa dukk lokacin da ka yi masa salati.
KADAN DAGA CIKIN LADA DA SAKAMAKON SALATI GA ANNABI ﷺ
1-Wanda yayi masa salati guda daya Allah zai yi masa guda goma.
@[صحيح : رواه مسلم].
2-Manzon Allah ﷺ zai mayar da sallama da salati ga dukkan wanda yayi masa.
@[حسن : رواه أحمد (٢٥٧/٢) ، وأبو داود(٢٠٤١) ، وحسنه الألباني في " صحيح الترغيب" ( ١٦٦٦)]
3-Allah yana sanyawa a isar da salatinka zuwa ga Manzon Allah ﷺ.
@[صحيح : رواه رواه النسائي في " عمل اليوم والليلة"(٦٦) ، وابن حبان في " الصحيح" (٩١٤) ، وصححه الألباني في "صحيح الترغيب"(١٦٦٤)].
4-Ana bujirowa Annabi ﷺ salatin dukkan wanda yayi salati a gare shi.
@[صحيح : رواه أحمد(٤/٧) ، وأبو داود(١٠٤٧) ، وابن ماجه (١٠٨٥) ، وابن حبان (٩٠٧) ، والحاكم (٢٧٨/١) وصححه].
5-Wanda ya yawaita salati ga Manzon Allah ﷺ, Allah yana yaye masa bakin ciki kuma ya gafarta masa zunubansa.
@ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ : ﺣَﺪِﻳﺚٌ ﺣَﺴَﻦٌ ﺻَﺤِﻴﺢٌ . ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻟﻤﻨﺬﺭﻱ ﻓﻲ ( ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ) ، ﻭﻛﺬﺍ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﻓﻲ " ﺍﻟﻔﺘﺢ " ( 11/168 ) ، ﻭﺃﺷﺎﺭ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻓﻲ " ﺍﻟﺸﻌﺐ " ( 2/215 ) ﺇﻟﻰ ﺗﻘﻮﻳﺘﻪ ، ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ " ( 1670 ) ﻭﻏﻴﺮﻩ
6-Wanda ya yawaita salati ga Annabi ﷺ,yana samun ceton Annabi ﷺ, a gobe alqiyama.
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﻗﺎﻝ : ﺣﺪﻳﺚ ﺣﺴﻦ )
7-Mai yawaita salati ga Annabi ﷺ, yana samu lada mai yawa domin,za'a rubuta masa lada goma kuma a kankare masa zunubai guda goma kuma a daukaka darajarsa sau goma.
@صحيح الجامع
Wannan kadan kenan daga cikin romon lada da ake samu cikin yiwa Manzon Allah ﷺ salati.
Allah ya bamu ikon yi masa salati ko kuma koyi da shi acikin dukkan ibadar mu.
« ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺻﻞِّ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻴﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ . ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺑﺎﺭِﻙ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺑﺎﺭﻛﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ »