
08/05/2025
RIKICIN INDIYA DA PAKISTAN....
Bayan da kasar Pakistan ta samu nasarar kakkabo jiragen yakin indiya wadanda ta siyo daga kasar France, wanda hakan ya janyo hannayen jarin kamfanin Dassault Rafale s**a faɗi a kasuwa...
A daren jiya Indiya ta harba Jirage marasa Matuki DRONES wadanda ta siyo daga kasar Isra'ila sai dai kasar Pakistan ta samu nasarar kakkabo DRONES sama da 25 da aka harba mata...
DRONES din da ake kira da HAROP DRONES sun kasance daga cikin drones mafiya haɗari da kasar Isra'ila take kerawa...
Indiya ta kai farmakin ne zuwa garuruwan Rawalpind, Gujranwala, Attock, Chakwal, Lahore, Bahawalpur, Miano, Chhor, Karachi sai dai kusan dukkan drones din an samu nasarar kakkabo su sakamakon kwarewa da sojojin Pakistan s**a nuna...
Har zuwa yau alhamis Pakistan bata mayar da martanin hari ga kasar Indiya ba, amma ana kyautata zaton zata kai mummunan hari da zai girgiza kasar Indiya....
To Madallah....