29/05/2026
DR YAKUBU ADAMU A TAKAICHE
Dan asalin Giade, an haife shi a Gwabba, ya tashi a Ilelah da Karofin Madaki
An tabbatar da Yakubu Adamu, PhD, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) mai mulki a Jihar Bauchi domin zaɓen shekarar 2027.
Dr. Yakubu bai samu wannan matsayi cikin kuskure ko sa’a kawai ba. Cikin tawali’u da nutsuwa ya gina kansa har ya kai wannan matsayi mai daraja, duk da kasancewarsa matashi daga gida mai sauƙin rayuwa.
Yana da ƙwarewa sosai wajen shugabanci da gudanarwa, kasancewar ya yi aiki a harkar banki na tsawon lokaci. Ya fara aikin banki ne daga ƙaramin matsayi, amma cikin ƙanƙanin lokaci ya riƙa hawa matakai daban-daban har ya kai matsayin jagoran sashen kula da gwamnati a yankin Arewa maso Gabas da kuma Manajan Bunƙasa Harkokin Kasuwanci na Polaris Bank a Bauchi.
Yakubu Adamu, PhD, shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki na Jihar Bauchi da ya gabata nan kusa. Ya yi murabus daga muƙaminsa a watan Afrilun 2026 domin mayar da hankali kan burinsa na neman kujerar gwamna.
Shi ɗan asalin ƙauyen Gulbun ne da ke Gundumar Doguwa a Ƙaramar Hukumar Giade ta Jihar Bauchi. An haife shi a unguwar Gwabba da ke cikin garin Bauchi a ranar 12 ga Agustan shekarar 1980. Ya taso tsakanin Gwabba inda aka haife shi, Ilelah inda ya fara karatun firamare, da kuma Karofin Madaki inda ya ci gaba da rayuwarsa.
Ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Kofar Fada daga shekarar 1986 zuwa 1992.
Bayan kammala makarantar firamare, ya halarci Pilot Junior Secondary School daga 1992 zuwa 1995 domin karatun sakandare na ƙasa, sannan ya wuce Government Science Secondary School Toro daga 1995 zuwa 1998 domin karatun sakandare na gaba da ƙasa.
Ƙishirwar neman ilimi da faɗaɗa tunaninsa bai tsaya a nan ba, domin ya samu gurbin karatu a Kwalejin Fasaha ta Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi, inda ya yi shirin Advanced Level tsakanin shekarar 1999 zuwa 2001.
A shekarar 2001, ya samu gurbin karatu a babbar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) Bauchi, inda ya samu digirin farko na B.Tech a fannin Gudanar da Kasuwanci a shekarar 2006. Daga bisani ya koma wannan jami’a a shekarar 2008, inda ya samu digirin MBA a shekarar 2013.
Neman iliminsa bai tsaya nan ba. Dr. Adamu ya kai kololuwar tafiyarsa ta ilimi bayan ya samu wani digirin Masters a fannin Finance, Investment and Banking daga International University of Bamenda da ke Jamhuriyar Kamaru tsakanin 2014 zuwa 2016. Daga baya ya koma jami’ar inda ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanarwa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.
Bincikensa da rubuce-rubucensa a fannin kuɗi da bunƙasa tattalin arziki sun ƙara tabbatar da shi a matsayin mutum mai ilimi da ƙwarewa sosai da kuma mutunci a idon jama’a.
AIKINSA NA ƘWARARRU
Aikinsa ya fara ne a First City Monument Bank (FCMB) a shekarar 2008, inda ya yi aiki har zuwa 2013 yana ƙara gogewa a harkar banki. Ƙwarewarsa da kwarewa wajen tafiyar da harkokin kuɗi ne s**a kai shi wani muhimmin matsayi a Polaris Bank, inda ya yi aiki daga 2013 zuwa 2023 har ya kai matsayin Regional Manager.
Ya yi aiki a matsayin Team Lead, Public Sector (Northeast) a Polaris Bank Limited daga 2019 zuwa 2021; Business Development Manager a Skye Bank Plc Bauchi daga 2015 zuwa 2019; Head of Branch Retail a Skye Bank Plc Bauchi daga 2012 zuwa 2015; sannan Marketing Officer a First City Monument Bank daga 2008 zuwa 2012.
Dr. Yakubu Adamu mamba ne na Nigerian Institute of Management (Chartered), da Chartered Institute of Economics, da Chartered Institute of Bankers of Nigeria, da kuma Chartered Institute of Loan and Risk Management.
SHIGOWARSA SIYASA
Shigowar Yakubu Adamu, PhD cikin siyasa ya fara ne lokacin da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya naɗa shi a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki a shekarar 2023. Duk da cewa wannan naɗi ne ya fito da shi fili a siyasa, tun kafin hakan Yakubu ya taka muhimmiyar rawa wajen yakin neman zaɓen karo na biyu na gwamnan.
Doguwar gogewarsa a harkar banki ta ba shi cikakken tushe wajen tafiyar da harkokin kuɗi, aiwatar da manufofi da bunƙasa tattalin arziki a matakin yanki. Matsayansa daban-daban a harkar banki sun ƙara ba shi fahimta sosai kan tsarin kuɗi, ƙwarewar da ya yi amfani da ita yadda ya k**ata lokacin da yake Kwamishinan Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki.
Dr. Yakubu Adamu ya kasance daya daga cikin ginshiƙan gwamnatin Gwamna Bala Mohammed, musamman wajen aiwatar da shirye-shiryen My Project 1 da My Project 2 da aka ƙaddamar domin bunƙasa Jihar Bauchi. Ya nuna nagarta, hangen nesa da jajircewa wajen kawo sauyi mai amfani ga al’umma.
Yana da aure tare da ’ya’ya. Daga cikin abubuwan sha’awarsa akwai wasan ƙwallon ƙafa, karatu da bincike. Haka kuma Dr. Yakubu yana riƙe da manyan sarautun gargajiya na Wazirin Giade da kuma Sardaunan Gulbun.
Rubutawa: Abdul Ahmad Burra
Fassarawa: BAUCHI YOUTH COALITION FOR GOOD GOVERNANCE