10/08/2026
KANO TA AREWA: Sanata Barau Ya Ƙara Ƙarfi A Harjar Lafiya, Ya Samar Da Magunguna Kyauta Ga Jama'a
Al’ummar Kano Ta Arewa na ci gaba da samun tallafin da ya shafi rayuwarsu, yayin da Sanata Dr. Barau I. Jibrin (Maliya) ya samar da magunguna kyauta domin amfanin al’ummar ƙananan hukumomi 13 da yake wakilta.
Matakin na daga cikin shirye-shiryen tallafa wa jama’a da rage musu matsin lamba, musamman waɗanda ke fuskantar wahalar samun kuɗin sayen magani.
A yayin da samun ingantaccen magani ke da muhimmiyar rawa wajen kare lafiyar al’umma, wannan tallafi na Sanata Barau ya zo a matsayin abin da zai taimaka wa iyalai da dama wajen samun magungunan da suke buƙata.
Sanata Barau ya sake nuna cewa wakilci ba ya tsaya kan ayyukan Majalisa kawai, domin yana ƙoƙarin ganin ayyukan da ake yi sun shafi rayuwar jama’a kai tsaye.
Masu bibiyar ayyukan wakilan jama’a na cewa irin wannan tsari na ƙara bayyana muhimmancin samun wakili da ke mai da hankali kan abubuwan da s**a shafi lafiya da jin daɗin al’umma.
Ga al’ummar Kano Ta Arewa, samar da magungunan kyauta ga ƙananan hukumomi 13 na ƙara zama wani abin tunawa a fannin tallafa wa jama’a.
Sanata Barau ya sake tabbatar da cewa: Wakilci na gaskiya shi ne wanda jama’a ke jin amfaninsa a rayuwarsu.