06/09/2025
ZANNAN ANKA FOUNDATION
SANATA ABDUL'AZIZ YARI (MARAFAN SOKOTO), YA JAGORANCI GABATAR DA LITTAFIN "WHERE I STAND" NA SHEIKH ABUBAKAR MAHMOUD GUMMI, WANDA D.R JALO JALINGO YA FASSARA ZUWA LARABCI.!
Mai girma Tsohon Gwamnan jihar zamfara kuma Sanatan Shiyar zamfara ta Yamma, His Excellency Sanata Al-sheikh (Dr), Abdul'aziz Abubakar Yari (Marafan Sokoto), ya Jagoranci gabatar da littattafin WHERE I STAND Na Marigayi Sheikh Abubakar Mahmood Gummi, wanda Shugaban majalisar malamai na kungiyar izala ta ƙasa, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, ya Fassara zuwa Harshen larabci.
Taron Kaddamar da Littafin wanda kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Waikamatis Sunnah ta kasa, karkashin jagorancin Shugaban ta Kuma Shugaban haɗinkan kungiyoyin ahlus-sunnah na afrika, Fadilatush-Sheik Imam (Dr), Abdullahi balalau ta shirya a ɗakin taro na Ummaru musa "Ƴar aduwa dake Murtala Square a garin kaduna dake shiyar arewa maso yammacin Najeriya.
Mai girma Shugaban kasar Najeriya, His Excellency, Sen. Asiwaju Bola Ahmad Tinubu GCFR, wanda mai girma Gwamnan jihar kaduna, H.E Sen. Malan Uba Sani ya wakilta, Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, H.E Malam mani mummuni, Tsohon gwamnan jihar kaduna, H.E Alhaji Mukhtar Ramalan Yaro, Manyan malaman addinin Musulunci na kungiyar Shuwagabannin majalisar zartaswa dana majalisar malamai da majalisar "Ƴan agajin na cikin muhimman Mutanen da s**a shaidi wannan taro a garin na kaduna.
1. Imam Abdullahi Balalau
2. Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe
3. Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun
4. Dr. Ahmad Abubakar Gumi
5. Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya
6. Dr. Tukur Adam Almanar.
7. Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan.
8 Assoc. Prof Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemu
9. Prof. Zubairu Abubakar Madaki.
10. Dr. Abdulkadir Ismail Kumo.
Muna Rokon Allah Madaukakin sarki ya Sakamasa da mafificin Alkhairin ya sanya a mizani na lada yabamu sakamako da Al-jannah madaukakiya albarkar wannan aiki na alkhairi amin.