26/06/2026
DAGA AL-QUR'ANI KAI TSAYE: SU WAYE MATA NAGARI?
Sheikh Dr. Mansur Isah Yelwa Hafizahillah ya ce:
Akwai wasu mutane da suke ganin
nagartar mace tana auna ne da yawan sallarta,
Yawan azuminta, yawan sadakarta ko
Kuma yawan hajjin da ta yi.
Amma Allah Madaukakin Sarki ya nuna
cewa akwai wani babban ma'auni
Da mutane da yawa suke mantawa da shi.
Allah Ya ce:
Arrijalu qawwamuna alan nisa...
Sannan Ya ci gaba da cewa:
Fassalihatu qanitat...
Malam ya ce:
Ka lura, Allah da kansa ya fara bayanin waye mace ta gari.
Ya ce:
Fassalihatu — Mata nagari.
Sai Ya bayyana sifarsu:
Qanitat — Masu biyayya.
Malam ya ce,
Allah bai fara da cewa mata nagari su ne
masu yawan nafila ba, ko masu yawan azumi ba,
Ko masu yawan Umara ba.
Sai dai Ya fara da sifar biyayya da mutunta
Tsarin da Allah Ya kafa a cikin aure.
Saboda haka, idan ana son a san
wace ce mace ta gari a wurin Allah,
ba wai kawai a duba yawan ibadarta ba.
A duba yadda take kallon matsayinta a cikin gida.
A duba yadda take mu'amala da mijinta.
A duba yadda take girmama umarnin Allah a rayuwar aurenta.
Malam ya ce:
Akwai mace mai yawan ibada,
Amma tana raina tsarin da Allah Ya kafa.
Akwai kuma mace mai sauƙin hali,
Mai biyayya, mai kiyaye hakkokin gidanta,
Wadda Allah Ya sanya cikin jerin "Fassalihatu Qanitat."
Don haka, Musulunci bai zo ya tauye mace ba.
A'a, ya zo ne ya ɗaukaka ta, ya ba ta matsayi,
ya nuna mata hanyar da za ta samu yardar Allah da Aljannah.
Duk wanda yake son sanin ma'aunin
nagarta a wurin Allah, to ya koma ga abin da Allah Ya faɗa,
Ba abin da ra'ayin mutane ko zamani suke faɗa ba.
Allah Ya sa mu fahimci addininmu yadda ya kamata.
🤲 Allah Ka ƙara wa Sheikh Dr. Mansur Isah Yelwa lafiya,
albarka da tsawon rai a kan alkhairi.
Ka saka masa da aljannar Firdausi
saboda ilmantar da al'umma. Amin.
🤲 Masu sharing wannan saƙo,
Allah Ya saka muku da alkhairi.
Ya gyara mana zukatanmu,
Ya sa mu karɓi gaskiya idan ta zo mana,
Ya ba maza da mata ikon yin rayuwa bisa
Koyarwar Al-Qur'ani da Sunnah.
Amin.
Addinu Annasiha✍️