20/05/2026
DA DUMI-DUMI: Senator Shehu Buba Umar Ya Janye Daga Takarar Gwamnan Bauchi a Jam'iyyar APC
Sanatan Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar, ya sanar da janyewarsa daga takarar gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC gabanin zaɓen fidda gwani da aka shirya gudanarwa ranar 21 ga Mayu, 2026
A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, Sanatan ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin nuna rashin amincewarsa da yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar a jihar, musamman abin da ya kira karya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, dokar zaɓe ta 2026, kundin tsarin APC na 2022 da kuma ƙa’idojin jam’iyyar.
Sanarwar ta kuma ce tun kafin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a ranar 19 ga Afrilu, 2026, jam’iyyar APC a Bauchi ta shiga rikicin shugabanci, musamman a wasu muhimman muƙamai na kwamitin gudanarwa na jihar kamar Sakataren Jiha da Sakataren Tsare-tsare.
Sanata Shehu Buba Umar ya ce ya janye daga takarar ne a matsayin zanga-zangar siyasa, yana mai nuna damuwa kan yadda rikice-rikicen cikin gida ke barazana ga haɗin kan jam’iyyar a Jihar Bauchi.