A-20 For Makama Babba 2027

A-20 For Makama Babba 2027 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from A-20 For Makama Babba 2027, Political Party, 1 GONGOLA Street, BEHIND OLD DASS, , PARK, AFTER MARYAMA HOTEL NEW GRA, , , BAUCHI, Bauchi.

A-20 For Makama Babba 2027 is a broad-based alliance across the 20 LGAs of Bauchi State, committed to sustaining good governance, rebuilding public trust, promoting unity, grassroots mobilization, and supporting another APC-led government in 2027.

SAKON TAYA MURNA DA FATAN ALKHAIRI GA HIS EXCELLENCY MUHAMMAD ABDULLAHI ABUBAKAR (SAN) A BIKIN CIKAR DEMOKURAƊIYYA SHEKA...
12/06/2026

SAKON TAYA MURNA DA FATAN ALKHAIRI GA HIS EXCELLENCY MUHAMMAD ABDULLAHI ABUBAKAR (SAN) A BIKIN CIKAR DEMOKURAƊIYYA SHEKARU 27

A madadin mambobi da magoya bayan A-20 FOR MAKAMA BABBA 2027, muna miƙa saƙon taya murna da fatan alkhairi ga Muhammad Abdullahi Abubakar (SAN) bisa zagayowar cikar dimokuraɗiyya shekaru 27 a Nijeriya.

Wannan rana ta kasance abin tunawa ga irin gwagwarmayar da aka yi domin tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya, adalci, da bai wa al’umma damar zaɓar shugabanninsu cikin ‘yanci. A irin wannan lokaci, ya dace a yaba wa shugabanni masu hangen nesa da s**a bayar da gudummawa wajen bunƙasa tsarin mulki da ci gaban al’umma.

His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar (SAN), wanda ya jagoranci Jihar Bauchi daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jagororin da s**a bayar da tasu gudummawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, bin doka da oda, da kuma gudanar da mulki bisa tsarin gaskiya da rikon amana.

A wannan muhimmin lokaci na cikar dimokuraɗiyya shekaru 27, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima, basira da ƙarfin guiwa domin ci gaba da hidimtawa al’ummar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya. Haka kuma muna addu’ar Allah Ya albarkaci tafiyarsa ta siyasa da shugabanci, Ya sanya alkhairi da nasara a dukkan ayyukansa na al’umma.

Dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne da shugabanni nagari, masu hangen nesa da kishin jama’a.

Allah Ya ƙara ɗaukaka Makama Babba, Ya sa gaba ta fi baya, Ya kuma ci gaba da kare Nijeriya da Jihar Bauchi.

Barka da Cikar Dimokuraɗiyya Shekaru 27!

Daga: A-20 FOR MAKAMA BABBA 2027
Muna Goyon Bayan Nagartaccen Jagoranci Domin Ci Gaban Bauchi.

A visionary leader, with heart so bright      His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar (SAN)Shining example for Us.
09/06/2026

A visionary leader, with heart so bright
His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar (SAN)

Shining example for Us.

MUNA LAYIN MAKAMA BABBA A tarihin siyasar Bauchi, His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar (SAN) ya kasance ɗaya daga ...
09/06/2026

MUNA LAYIN MAKAMA BABBA

A tarihin siyasar Bauchi, His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar (SAN) ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin da s**a yi ƙoƙarin aiwatar da manufofin gyaran tsarin gwamnati, lafiya, noma, ilimi da ci gaban tattalin arziki domin amfanin al'ummar jihar Bauchi.

Idan za a yi adalci wajen nazarin tarihin Shubancin His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar (SAN) na baya, ya kamata a kalli shirin verification a matsayin wani yunƙuri na gyara tsarin aikin gwamnati da kare kuɗaɗen jama'a. Duk da cewa irin waɗannan sauye-sauye kan fuskanci ƙalubale a wasu ɓangarori, sakamakon da aka bayyana na gano dubban ma'aikatan bogi ya nuna cewa manufar shirin ita ce tabbatar da gaskiya da inganta tattalin arzikin jihar Bauhi.

Media Team A-20 For Makama Babba 2027

More Bless 💗

ME YA SA AKA YI VERIFICATION?Lokacin da gwamnatin Muhammad Abdullahi Abubakar ta fara aikin tantance ma'aikata a shekara...
08/06/2026

ME YA SA AKA YI VERIFICATION?

Lokacin da gwamnatin Muhammad Abdullahi Abubakar ta fara aikin tantance ma'aikata a shekarar 2015/2016, manufar ba wai cutar da ma'aikata ba ce, sai dai gano ma'aikatan bogi (ghost workers) da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen gwamnati suna zuwa ga ma'aikatan da s**a cancanta. Rahotanni sun nuna cewa an gano dubban ma'aikatan bogi a tsarin albashin jihar, lamarin da ke janyo asarar kuɗaɗen al'umma.

Har ila yau, gwamnatin ta bayyana cewa an gano sama da ma'aikatan bogi 6,000 a sakamakon wannan tantancewa, kuma an ce hakan ya taimaka wajen rage almubazzaranci da kare dukiyar jama'a.

Saboda haka, daga mahangar shugabanci nagari, verification ba hukunci ba ne ga ma'aikata, illa wata hanya ce ta tabbatar da gaskiya, adalci da kuma inganta tsarin gudanar da gwamnati.

Media Team.
Akwai warwara Insha Allah

LOKACIN HAƊIN KAI YA YI DOMIN MAKOMAR 'YA'YANMUDA YARDAR ALLAH LOKACI YA ZO NA SAMUN DAMAR GYARARRAKI DA TABBATAR DA GOY...
08/06/2026

LOKACIN HAƊIN KAI YA YI DOMIN MAKOMAR 'YA'YANMU

DA YARDAR ALLAH LOKACI YA ZO NA SAMUN DAMAR GYARARRAKI DA TABBATAR DA GOYON BAYA GA IYAYEN KASA, A-20 ZATA YI AIKI WAJEN SAMAR DA DAIDAITO GA AL'UMA DA SHUGABANNIN DA SUKE JAGORANTAR SU.

KOWA YA CE ALHAMDULILLAH

Muna yi wa His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar SAN fatan alkhairi, nasara da karin lafiya. Allah yakara masa hiki...
08/06/2026

Muna yi wa His Excellency Muhammad Abdullahi Abubakar SAN fatan alkhairi, nasara da karin lafiya. Allah yakara masa hikima, basira da juriyar jagoranci domin ci gaban Jihar Bauchi. Allah Ya sa dukkan manufofinsa na alheri su tabbata, Ya kuma ci gaba da zama abin koyi wajen gaskiya, adalci da hidimtawa al'umma.
Amin.

Media Team

Address

1 GONGOLA Street, BEHIND OLD DASS, , PARK, AFTER MARYAMA HOTEL NEW GRA, , , BAUCHI
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when A-20 For Makama Babba 2027 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share