17/07/2026
SAƘON KAMFEN – MUHAMMAD ABDULLAHI ABUBAKAR, SAN
BAUCHI SABUWA TA HANYAR KWAREWA DA GOGEWA
Bismilahar Rahmanir Rahim.
'Yan uwa al'ummar Jihar Bauchi,
Lokaci ya yi da za mu sake haɗuwa domin gina Bauchi mai ci gaba, adalci da wadata. Muhammad Abdullahi Abubakar, SAN, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, ya sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi domin ci gaba da yi wa al'umma hidima. Ya bayyana aniyarsa ta neman takarar gwamna a 2027 tare da mataimakinsa Dattijon kirki Hon faruq Mustapha kuma rahotanni sun nuna sun shiga wannan fafatawa ta jam'iyyar APC
Mun yi imani cewa kwarewa, gaskiya, shugabanci nagari da hangen nesa su ne ginshiƙan ci gaban kowace al'umma.
Abin da muke fata ga Bauchi sune Kamar Haka:
Inganta ilimi da kiwon lafiya.
Ƙarfafa noma da samar da ayyukan yi ga matasa.
Gina da gyaran hanyoyi da sauran ababen more rayuwa.
Tallafa wa mata da matasa ta hanyar bunƙasa kasuwanci, inganga tsaro da tabbatar da adalci wa kowa
Muna kira ga dukkan al'ummar Bauchi da su shiga wannan tafiya cikin lumana, mutunta juna, da bin doka. Mu gudanar da kamfen cikin mutunci tare da bayyana manufofi da shirye-shiryen da za su amfani jama'a.
Muhammad Abdullahi Abubakar, SAN Bauchi Sabuwa – Ci Gaba ga Kowa.
Bauchi Sabuwa Project
17th July 2026