Abban Bichi Support Group

Abban Bichi Support Group Domin samun cigaba da dimokradiyya fitar da gaskiya tare da wayar da kan mutane dan sanin yancinsu na zama yan kasa

Boom 💥 💥 💥 💥
12/04/2026

Boom 💥 💥 💥 💥

🔥 GUGUWAR SIYASA A KANO TA AREWA: AN SAMU MACE ‘YAR TAKARAR SANATA! 🔥A wani babban al’amari da ke girgiza fagen siyasa a...
08/04/2026

🔥 GUGUWAR SIYASA A KANO TA AREWA: AN SAMU MACE ‘YAR TAKARAR SANATA! 🔥

A wani babban al’amari da ke girgiza fagen siyasa a jihar Kano, wata fitacciyar mace mai ƙwazo da hangen nesa, Hajiya Uwani Muqaddas Bichi, ta fito fili tare da bayyana aniyarta ta tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Kano North Senatorial District!

💥 Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da siyasar Kano ke ƙara zafi, inda manyan ‘yan takara ke ci gaba da shirin fafatawa a zaɓe mai zuwa. Sai dai fitowar mace a wannan matsayi ya zama abin tarihi da kuma abin da ke ɗaukar hankalin al’umma baki ɗaya.

👀 Masu sharhi na cewa wannan ci gaba na iya sauya fasalin siyasa a Kano ta Arewa, musamman ganin yadda mata ke ƙara tasiri a harkokin shugabanci a Najeriya.

💬 Rahotanni daga yankin Bichi da sauran ƙananan hukumomi na Kano ta Arewa sun nuna cewa jama’a sun fara tattaunawa mai zafi kan wannan takara, inda wasu ke bayyana cikakken goyon baya, yayin da wasu ke kallon yadda lamarin zai kaya.

⚡ Wasu na ganin cewa wannan takara na iya zama babbar dama ga:
• Ƙarfafa shigar mata a siyasa
• Kawo sabbin manufofi masu anfani ga matasa
• Ƙara gasa mai inganci tsakanin ‘yan takara

📊 Duk da haka, ana sa ran cewa wannan mataki zai jawo gagarumar fafatawa daga sauran ‘yan siyasa da ke neman wannan kujera mai muhimmanci a Majalisar Dattawa.

🗣️ A nata bangaren, majiyoyi sun ce Hajiya Uwani Muqaddas Bichi na shirin gabatar da cikakken tsari da manufofinta nan ba da jimawa ba, wanda ake sa ran zai ƙara jan hankalin jama’a.

📌 Shin wannan mace za ta iya karya tarihi a Kano ta Arewa?
📌 Shin jama’a za su ba ta cikakken goyon baya?

👉 Ku kasance tare da mu domin samun sahihan bayanai da sabbin labarai kan wannan lamari mai ɗaukar hankali!

Kungiyar Abban Bichi Support Group ta bayyana jin daɗinta da gamsuwa bisa irin ayyukan alherin da matashi Hon. Nura MBS ...
30/10/2025

Kungiyar Abban Bichi Support Group ta bayyana jin daɗinta da gamsuwa bisa irin ayyukan alherin da matashi Hon. Nura MBS yake gudanarwa a yankin Bichi da kewaye.

Shugaban ƙungiyar, Ahmad Mustapha Mado, ya ce Hon. Nura ya kasance mutum mai kishin al’umma wanda ke yin aiki tukuru don inganta rayuwar jama’a, musamman matasa da mata, kamar yadda a koda yaushe Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi yake yi.

Ya ce, “Mun ga ayyukan ci gaba da taimakon al’umma da Hon. Nura MBS ke yi daga bayar da tallafi ga marasa galihu, zuwa gina hanyoyin samun ci gaba da tallafawa dalibai hakan ya nuna cewa yana da niyyar gaske wajen bunƙasa yankinmu.”

Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran ‘yan siyasa da su ɗauki darasi daga irin wannan matashi wanda ke aiki tukuru don jama’a, domin cigaban ƙaramar hukumar Bichi.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi addu’a ga Allah Ya ƙara wa Hon. Nura lafiya, natsuwa, da ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan alheri ga al’umma.

Sponsored…

Allah yayi maka chairman party APC bichi local governments Sirajo Shehu
27/10/2025

Allah yayi maka chairman party APC bichi local governments Sirajo Shehu

ABBAN BICHI SUPPORT GROUP TA YABA DA DATTIJO SIRAJO SHEHU (SIMAR) SLA — JIGON ALHERI🗓️ 05/10/2025A kowace al’umma, akwai...
05/10/2025

ABBAN BICHI SUPPORT GROUP TA YABA DA DATTIJO SIRAJO SHEHU (SIMAR) SLA — JIGON ALHERI

🗓️ 05/10/2025

A kowace al’umma, akwai wasu dattijai da suke zama ginshiƙi, fitila, da misali ga sauran jama’a. Dattijai masu natsuwa, hangen nesa, da zuciya mai cike da alheri. A yau, wannan yabo ya dace da Alhaji Sirajo Shehu (SIMAR) SLA, wanda ya sake tabbatar da cewa halin kirki da son jama’a su ne asalin siyasa ta gaskiya.

Abban Bichi Support Group ta bayyana cikakkiyar gamsuwa da jin daɗinta bisa gagarumin aikin alheri da wannan dattijo mai daraja ya aikata — ta hanyar saka mutum 600 daga cikin ’yan jam’iyyar APC cikin shirin ALHERI. Wannan mataki na SIMAR ya zama abin alfahari da koyi, kuma shi ne na farko cikin jerin ayyukan alheri da ya tanadar domin walwalar mambobin jam’iyyar a karamar hukumar Bichi.

A hakikanin gaskiya, abin da Sirajo Shehu ya aikata ya nuna irin zurfin tunani da tausayi da dattijo ke da shi. A maimakon ya tsaya a gefe yana kallo, ya ɗauki nauyin mutane da dama, ya sanya su cikin tsari mai fa’ida. Wannan aiki ne na zuciya mai imani, wanda ke nuna biyayya da koyi da jagoran cigaba, Hon. Engr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi (ABBAN ALHERI) — wanda ya kafa tafarkin taimako, ɗan adam, da kyautatawa cikin hikima da tawali’u.

Dattijo SIMAR ya bi wannan hanya da gaskiya, ba da niyyar nuna isa ba, amma da niyyar gina mutane da ɗaga darajar jam’iyya. Ya zama abin alfahari, wanda ya tabbatar da cewa siyasa ba wai rigima bace, amma hidima, tausayi, da sadaukarwa.

Abban Bichi Support Group ta bayyana cewa irin wannan aiki ya nuna irin biyayya da kauna da SIMAR yake da ita ga jam’iyya, ga al’umma, da kuma ga jagoransa Abban Alheri. Wannan ne dalilin da yasa ake cewa, “Wanda ya bi sahun alheri, alheri ne ke bin sawunsa.”

Kungiyar ta roƙi Allah (SWT) Ya kara masa lafiya, natsuwa, da tsawon rai mai albarka. Ya bashi ikon ci gaba da zama fitila ga sauran dattijai da matasa, domin ci gaban Bichi, jam’iyyar APC, da al’umma baki ɗaya.

A ƙarshe, Abban Bichi Support Group ta tabbatar da cewa tarihin wannan aiki zai zauna a zukata — saboda ba kowa ne ke iya sadaukar da lokaci, niyya, da dukiya wajen taimakon jama’a ba. Wannan shi ne abin da ake kira alheri mai ma’ana, wanda ya dace da mutum kamar Alhaji Sirajo Shehu (SIMAR) SLA.

Sirajo Shehu (SIMAR) SLA — dattijon kirki, jigon alheri, kuma mai bin sahun ABBAN ALHERI. Allah Ya saka da alheri, Ya kara masa daraja da lafiya.

---

🖋️ Saifullahi Real Verbs
Sakataren Yaɗa Labarai na Abban Bichi Support Group
A madadin mambobin ƙungiyar

Ubangidan fita kunya ❤️
15/09/2025

Ubangidan fita kunya ❤️

ABBAN BICHI SUPPORT GROUP TA YABI ENGR. ABUBAKAR KABIR ABUBAKAR BICHI KAN KADDAMAR DA AIKIN GIDAJEN BICHI MODERN CITY AB...
12/07/2025

ABBAN BICHI SUPPORT GROUP TA YABI ENGR. ABUBAKAR KABIR ABUBAKAR BICHI KAN KADDAMAR DA AIKIN GIDAJEN BICHI MODERN CITY


ABBAN BICHI SUPPORT GROUP na taya Engr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi murna da jinjina bisa wannan gagarumin tunani da hangen nesa na gina gidaje 2,000 a karkashin shirin Bichi Modern City. Wannan babbar gudummawa alama ce ta jajircewarsa wajen inganta rayuwar al’ummar Bichi da kewaye ta hanyar samar da mafita a zamanance, da kawo sauyin rayuwa mai sauki tare da dorewa a fannin gidaje.

Wannan aikin zai taimaka gaya wajen rage gibin rashin matsuguni, bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma kawo ci gaban birane a yankin. Muna taya Engr. Abubakar Kabir murna bisa wannan jajircewa da kishin ci gaban al'umma ta hanyar manyan ayyukan raya kasa.

ABBAN BICHI SUPPORT GROUP ta tsaya cak a bayan wannan aikin alheri kuma tana kira ga duk masu ruwa da tsaki da su bayar da gudummawarsu domin nasarar kammala shi. Tare zamu gina makoma mai haske da Ci gaba mai dorewa a karamar Hukumar Bichi.

Muna taya ka murna, Engr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi!
Bichi Modern City – Tarihi na Ci Gaba!

Sani da hannu,
Saifullahi (Real Verbs)
Jami’in Hulda da Jama’a (PRO),
ABBAN BICHI SUPPORT GROUP

PRESS RELEASEAn Kaddamar da Kwamitin Gudanar da Aikin Gidaje 2,000 a Bichi – Bichi Modern CityA wani babi na tarihi da c...
11/07/2025

PRESS RELEASE

An Kaddamar da Kwamitin Gudanar da Aikin Gidaje 2,000 a Bichi – Bichi Modern City

A wani babi na tarihi da ci gaba mai ma’ana ga al’ummar Bichi, Maigirma Dan Majalisar Tarayya, Engr. (Dr) Abubakar Kabir Abubakar Bichi, shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Tarayya, ya kaddamar da kwamitin dattawa guda Tara (9) domin lura da aiwatar da aikin gina sabbin gidaje 2000, karkashin babban shirin ci gaba na BICHI MODERN CITY.

Kwamitin zai yi aiki kafada da kafada da dan kwangila domin tabbatar da inganci, gaskiya da tsari a wannan aiki mai matukar muhimmanci da amfani.

Mambobin kwamitin sun hada da:

1. 🟢 Hon. Hamza Sule Maifata – Shugaban Kwamitin

2. 🟢 Hon. Sabo Iliyasu Saye – Sakataren Kwamitin

3. 🟢 DPO – Mamba

4. 🟢 OC DSS – Mamba

5. 🟢 HOD Works – Mamba

6. 🟢 Councillor Works – Mamba

7. 🟢 Engr. Isah Aliyu – Mamba

8. 🟢 Zaharaddin Kabir – Mamba

9. 🟢 Mal. Garba Tukur – Mamba

Shirin ya kai matakin da ba komai ya rage ba illa a kaddamar da aikin da yardar Allah. Wannan aiki ba wai kawai zai samar da mafita ga matsalar gidaje ba ne, har ma zai kawo gagarumin sauyi a zamantakewa, tattalin arziki da jin dadin al’umma.

Addu’armu ita ce:

Allah ya sanya aikin ya tafi cikin sauƙi da nasara tun daga farko har ƙarshe. Muna godiya ga Engr. (Dr) Abubakar Kabir Bichi – Abban Alkairi, wanda ya ci gaba da kasancewa ginshikin ci gaban Bichi. Allah ya saka masa da mafificin lada.

✍️ Saifullahi (Real Verbs)
Public Relations Officer (PRO),
ABBAN BICHI SUPPORT GROUP

09/07/2025

Address

Bichi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abban Bichi Support Group posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share