25/06/2026
📢 MUHIMMIYAR SANARWA GA DUKKAN MAMBOBIN YEMM
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Hukumar Youths Efforts and Mobilization Movement (YEMM) tana sanar da dukkan mambobi, magoya baya da masu fatan alheri cewa za mu gudanar da ziyara ta musamman zuwa gidajen marayu, gidajen gajiyayyu, gidajen gyaran hali da sauran wuraren da ke buƙatar tallafi da kulawa.
Wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarinmu na inganta rayuwar al'umma, ƙarfafa haɗin kai da kuma taimakon masu buƙata.
📅 Rana: Lahadi
🕑 Lokaci: Karfe 2:00 na rana daidai
📍 Wurin Taro: Gidan Alh. Sule Ara, APC Chairman Party, Bichi
Ana buƙatar dukkan mambobi su hallara cikin lokaci tare da nuna ladabi, haɗin kai da kishin hidimtawa al'umma.
"Taimakon al'umma alhakin kowa ne."
YEMM – TOGETHER WE MOVE
Abubakar Sulaiman
Chairman, YEMM
Bashir Adamu (Donbee)
Director General, Media, YEMM