Comrade Nasir Abdullahi Gwandu Media Team

Comrade Nasir Abdullahi Gwandu Media Team Aslm. Fatar kowa na cikin koshin lafiya Allah yasa hakan ameen. Kamar yada kowa yasani muna cigaba da

SANARWA TA MUSAMMANAssalamu Alaikum wa Rahmatullah.Ni, Cmrd. Nasir Abdullahi Mai Gwandu, Aspirant of Birnin Kebbi North,...
15/05/2026

SANARWA TA MUSAMMAN

Assalamu Alaikum wa Rahmatullah.

Ni, Cmrd. Nasir Abdullahi Mai Gwandu, Aspirant of Birnin Kebbi North, tare da sauran abokan tafiyata, magoya baya da matasa masu kishin cigaban jam’iyyar mu ta ADC, muna mika godiya ta musamman ga Allah SWT sannan muna nuna cikakken biyayya da ladabi ga jagororinmu da shugabannin jam’iyya bisa irin kokarin da suke yi domin tabbatar da hadin kai, maslaha da cigaban jam’iyyar mu.

Bisa ga neman al’farmar jagoranmu, tsohon Minista Abubakar Malami, SAN, tare da kokarin kwamitin sulhu (Reconciliation Committee) na jam’iyya, mun amince da janyewa daga takarar neman kujerar Dan Majalisar Birnin Kebbi North domin tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da kuma domin kara karfin jam’iyyar ADC gaba daya.

Wannan mataki ya samo asali ne saboda bukatar samar da fahimtar juna, maslaha da hadin kai tsakanin ‘yan takara da shugabannin jam’iyya domin kara karfin jam’iyyar ADC zuwa babban zaben shekarar 2027.

Muna amfani da wannan dama wajen mika godiya ta musamman ga dukkan shugabanni, magoya baya, matasa, abokai da al’ummar da s**a tsaya tare da mu tun daga farkon wannan tafiya. Goyon bayan ku, addu’o’in ku da kaunar da kuka nuna sun kasance babban abin alfahari da karfafa gwiwa a gare mu.

Haka kuma, muna kira ga daukacin matasa da magoya bayanmu da su kasance masu biyayya, hakuri da ladabi ga shugabanni, sannan mu ci gaba da hada kai da jajircewa wajen neman jama’a domin tabbatar da nasarar jam’iyyar mu ta ADC a shekarar 2027, Insha Allah.

Muna addu’ar Allah SWT Ya kara hada kanmu, Ya bawa jam’iyyar mu nasara, Ya kuma zabi mafi alkhairi ga al’ummar Birnin Kebbi North da Najeriya baki daya.

Nagode sosai.

Cmrd. Nasir Abdullahi Mai Gwandu
Aspirant, Birnin Kebbi North

Mai gwandu for birnin Kebbi North Insha Allah 2027🤝
08/05/2026

Mai gwandu for birnin Kebbi North Insha Allah 2027🤝

Assalamu Alaikum. Juma’a mubarak zuwa ga al’ummar mazabar Birnin Kebbi North baki ɗaya.Ina roƙon Allah Ya sanya wannan r...
01/05/2026

Assalamu Alaikum.

Juma’a mubarak zuwa ga al’ummar mazabar Birnin Kebbi North baki ɗaya.

Ina roƙon Allah Ya sanya wannan rana mai albarka ta zamo sanadin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a tsakaninmu.

Allah Ya albarkaci jihar Kebbi da ƙasa baki ɗaya.

Cmrd. Nasir Abdullahi Mai Gwandu
Aspirant, Birnin Kebbi North

Alhamdulillah, Munsamu kai ziyara tare da tattaunawa mai ma’ana da wasu shugabannin ƙungiyoyin matasa dake cikin mazabar...
23/04/2026

Alhamdulillah, Munsamu kai ziyara tare da tattaunawa mai ma’ana da wasu shugabannin ƙungiyoyin matasa dake cikin mazabar Marafa Ward, inda aka tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi cigaban al’umma, musamman matasa.

Dan takarar kujerar Dan Majalisa mai wakiltar Birnin Kebbi North, Cmrd. Nasir Abdullahi Mai Gwandu, ya ja hankalin al’umma, musamman matasa, kan muhimmancin tashi tsaye domin fuskantar ƙalubalen da ke gaban mu. Ya kuma ƙarfafa muna gwiwa da mu rungumi haɗin kai, ilimi, da koyon sana’o’i a matsayin hanyoyin gina makoma mai kyau.

Haka kuma, ya bayyana kudurinsa na zama wakili nagari wanda zai tsaya tsayin daka wajen kawo mafita ga matsalolin yankin, tare da kare muradun al’umma a kowanne mataki.

A ƙarshe, ya nemi goyon baya, addu’a, da kuma ci gaba da wayar da kai domin ganin wannan tafiya ta kai ga nasara, tare da samar da ingantaccen cigaba ga Birnin Kebbi North.

Mai Gwandu Media Team

Ziyarar Bangirma a Mazabar Makera WardA yau, ɗan takarar kujerar Dan Majalisa ta Birnin Kebbi North, Cmrd. Nasir Abdulla...
23/04/2026

Ziyarar Bangirma a Mazabar Makera Ward

A yau, ɗan takarar kujerar Dan Majalisa ta Birnin Kebbi North, Cmrd. Nasir Abdullahi Mai Gwandu, ya kai ziyarar bangirma a Mazabar Makera Ward, inda ya gana da Shugaban Jam’iyya na mazabar tare da Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Birnin Kebbi Local Government, da wasu shuwagabannin jam’iyya na wannan mazabar.

An tattauna batutuwa masu muhimmanci kan cigaban jam’iyya da haɗin kai, inda shugabannin s**a nuna jin daɗinsu da girmamawa ga hangen nesa na wannan matashin, tare da bayyana goyon bayansu.

Haka kuma, ya kai ziyara ga wasu matasa da tsofaffi a cikin gari domin ƙarfafa alaƙa da haɗin kai.

A ƙarshe, muna roƙon Allah Ya ba Mai Gwandu sa’a da nasara a 2027.

Mai Gwandu Media Team

ZIYARAR MAZABAR MAURIDA WARDA ranar Juma’a, 17 ga watan April, 2026, ɗan takarar kujerar ɗan majalisar jihar Kebbi ta Ar...
23/04/2026

ZIYARAR MAZABAR MAURIDA WARD

A ranar Juma’a, 17 ga watan April, 2026, ɗan takarar kujerar ɗan majalisar jihar Kebbi ta Arewa (Birnin Kebbi North), Cmrd. Nasir Abdullahi Mai Gwandu, ya kai ziyarar aiki a mazabar Maurida Ward.

Ziyarar ta kasance mai matuƙar muhimmanci, inda ya zagaya ƙauyuka da dama domin ganawa kai tsaye da al’umma, sauraron koke-kokensu tare da jin buƙatunsu domin samar da ingantaccen wakilci idan aka ba shi dama.

Haka kuma, a cikin wannan ziyara, ya samu halartar wani ɗaurin aure a yankin, inda ya taya ma’auratan murna tare da yi musu fatan alheri da zaman lafiya mai ɗorewa.

Al’ummar mazabar sun nuna farin ciki da tarba mai kyau, tare da bayyana goyon bayansu da addu'oi ga wannan tafiya.

Allah ya qara Yima jagora Yakuma baka nasara ameen.

Mai Gwandu Muryar Jama’a!

© Mai Gwandu Media Team

Alhamdulillah, mun samu damar kai ziyarar bangirma da gaisuwa ga daya daga cikin dattawan jam’iyyarmu mai albarka, wato ...
14/04/2026

Alhamdulillah, mun samu damar kai ziyarar bangirma da gaisuwa ga daya daga cikin dattawan jam’iyyarmu mai albarka, wato Alh. Ubale, a gidansa.

Wannan ziyara ta samu jagorancin Dan takarar kujerar Dan Majalisar Birnin Kebbi ta Arewa, Hon. Nasir Abdullahi Mai Gwandu, tare da tawagarsa domin gaisawa da kuma karɓar shawarwari daga wannan babban dattijo.

Ziyarar ta gudana cikin yanayi na girmamawa da mutunta juna, inda muka samu kyakkyawar tarba tare da addu’o’i da kuma ƙarin kwarin gwiwa domin ci gaba da wannan tafiya da muke yi.

Muna miƙa godiya ta musamman ga Alh. Ubale bisa karamci da goyon bayan da yake bai wa wannan tafiya. Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.

Mai Gwandu Media Team

14/04/2026

Ba gudu, ba ja da baya, za mu gudanar da babban taron ADC a yau - Atiku

Hukumomin Nijeriya sun yi barazanar soke shaidar mallakar filin Rainbow da muka tsara gudanar da babban taron jam’iyyarmu ta ADC a Abuja in ji madugun adawa Atiku Abubakar

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da hango wa kanta faduwa a zabe sai ta koma neman duk wata hanyar da za ta kuntata wa jam’iyyar ADC. A cewarsa, hakan ya nuna ta rasa goyon bayan al’umma gaba daya. A bisa wannan dalilin ya ce ba gudu ba ja da baya, za su gudanar da taron ADC a yau don su zabi shugabannnin jam’iyyar domin babu wata dokar kasa da s**a karya.

Address

Kofa Sabuwa
Birnin-Kebbi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Comrade Nasir Abdullahi Gwandu Media Team posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share