Hisba Commission Yobe State - Fune Local Government Branch

Hisba Commission Yobe State - Fune Local Government Branch Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hisba Commission Yobe State - Fune Local Government Branch, Public & Government Service, Damagum, Fune Local Government, Yobe State, Damagum.

Wakilan Hukumar Hisba na Karamar Hukumar Fune Sun Kai Ziyara Ofishin Hisba na Jihar Yobe a DamaturuA wani bangare na kok...
26/05/2025

Wakilan Hukumar Hisba na Karamar Hukumar Fune Sun Kai Ziyara Ofishin Hisba na Jihar Yobe a Damaturu

A wani bangare na kokarin karfafa hadin gwuiwa tsakanin rassan hukumar Hisba a Jihar Yobe, wakilan hukumar Hisba na karamar hukumar Fune sun kai ziyara zuwa ofishin Hisbah na jihar Yobe da ke garin Damaturu.

Wannan tawaga ta kunshi Commander na Hisba na Fune, Mallam Umar Abdulmumini Dira, tare da Admin na hukumar, Mallam Aminu Abdullahi, da kuma shugaban tsaro (Head of Security), Mallam Ibrahim A. Usman. Sun samu tarba daga Mataimakin Kwamanda na Hisbah (Zone B), Mallam Muhammad Musa Potiskum, inda s**a gudanar da muhimmiyar tattaunawa akan al’amuran da s**a shafi ci gaban ayyukan Hisbah.

Bayan wannan ganawa, tawagar ta samu damar kai ziyara zuwa fadar mai martaba Sarkin Jajere, Alhaji Mai Hamza Buba Ibn, goyon baya daga masarautar. Haka kuma, sun ziyarci fadar Sarkin Ngelzarma, Alhaji Muhammad Zannah Mai Yeri Ibn Isah, inda s**a samu tarba mai kyau.

Wannan ziyara na daga cikin matakan karfafa zumunci da musayar kwarewa tsakanin rassa da matakin jiha na hukumar Hisba, da nufin inganta aikinta a tsakanin al’umma.

Hisbah Commission Yobe State - Fune Local Government Branch.
26th May, 2025.

Address

Damagum, Fune Local Government, Yobe State
Damagum

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisba Commission Yobe State - Fune Local Government Branch posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share