21/10/2025
Duk yadda za kayi da jaki sai ya ci kara !!!
Malam Bahaushe yayi gaskia da yace: Gwano ba ya jin warin jikinsa!
Yanzu kai tsabar rashin kunya irin ta ɗan IZALA, duk makauniyar soyayya da biyayya da kuke yiwa Ibnu Tamiyyah da Ɗan Abdulwahhabi, Bin Baz, Ibn Uthaimeen, Albany Bature, ba muce kunyi wa Annabi صلى الله عليه وسلم kishiya ba, sai mu zaku tuhuma da haka!??
Toh Bari in ɗan gutsuro maka wasu maganganun Shirka (kamar yadda kuke faɗa) da Taƙiyyuddini Addaƙuƙy yayi cikin wasu baitocin ta’aziyya da ya rubuta wa ma’asumin ku Ahmad ibn Taimiyyah randa ya mutu:
Ka duba (العقود الدرية في مناقب شيخ الاسلام ابن تيمية)
Yana cewa akan ibnu Taimiyyah:
يا واحد الدنيا الذي بعلومه ** يمتاز في الإسلام كل موحد
“ Ya kai tilo makaɗaicin duniya wanda da ilimominshi ne kowani mai kaɗaita ALLAH yake banbantuwa a Musulunci”
يا حامل الأعباء عن مستنصر ** يا كاشف الغماء عن مستنجد
“ Ya mai ɗauke nauyoyi ga mai neman taimako, Ya mai yaye baƙin ciki ga duk mai neman ɗauki”
Har yazo inda yake cewa:
يا خاتم العلماء صح بموتك ال ** خبر الذي يرويه كل مجود
Ya kai cika makin Malamai: Lallai akan mutuwar ka ne hadisin ɗauke ilimin da ko wani mahaddacin Hadisi yake rawaita, ya tabbata”
اليوم قبض العلم قولا واحدا ** من غير ما منع وغير تردد
“A Yau ranar mutuwar ka, tabbas ɗauke Ilimi a doron ƙasa ya tabbata, babu makawa babu shakka”
لو لم يكن ختم الأئمة أحمد ** بشرت أهل الخافقين بأحمد
“ ba dan Ahmad (Annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم ???) ya kasance cika makin limamai ba, da na yiwa mutanen gabas da yamna albishir da Ahmad (ibn Taimiyya)
يا من يروم له عديلا في الوري * قد رمت كالعنقاء مالم يوجد
“ Ya kai mai neman na biyun Ibnu Taimiyya a halitta, ka sani kamar kana neman tsuntsun (Anƙa’u) ne, dan ba’a halicci tsuntsun bama tukunna” !!
Kai yanzu da ace waɗannan naganganun sufaye ne s**a yabi Annabi صلى الله عليه وسلم dasu, da tuni kun fidda su daga musulunci, b***e kuma ace Shehu Ahmadu Tijjani ko Shehu Ibrahim inyass ko Sidi Abdulƙadir Jailani s**a yaba dasu !!!
Ga kashi a gindinku baku ji warin shi ba, sai na sufaye saboda tsabar ƙiyayyar bayin ALLAH da ta cika zukatan ku !!!
Imam Hassan Sheikh Dahiru Bauchi