03/10/2026
TAKAITACCEN TARIHIN ALHAJI BABA MALLAM WALI, mni
Alhaji Baba Malam Wali mni, shine dan takaran kujeran Gwamnan jihar Yobe a karkashin jam'iyyar APC
An haifi Alhaji Baba Mallam Wali a ranar 25 ga Disamba, 1958, a garin Nguru, Jihar Yobe, ga iyalan Mallam Shettima Modu da Hajiya Fatima Muhammad.
Ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Ngilewa, Nguru, daga shekarar 1965 zuwa 1972. Daga nan ya halarci Government Secondary School, Nguru, daga shekarar 1972 zuwa 1977, sannan ya yi karatun School of Basic Studies, Ahmadu Bello University (A.B.U.), Zaria, daga shekarar 1977 zuwa 1978.
A shekarar 1978, an ba shi gurbin karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya kammala karatun B.A. (Hons) a fannin Geography a shekarar 1981. Daga baya, a shekarar 1984, ya koma Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, domin ci gaba da karatu, inda ya samu Digirin M.Sc. a fannin Rural Development (Ci gaban Karkara) a shekarar 1986.
Karatuttuka da horarwar gudanarwa
A tsawon rayuwarsa ta aiki, Alhaji Baba Mallam Wali ya halarci kwasa-kwasai da tarukan karawa juna sani daban-daban kan harkokin gudanarwa, a Najeriya da kuma kasashen waje.
Daga cikin fitattun horarwar da ya samu akwai:
Senior Executive Course 36 na National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) a shekarar 2014, wanda ya kai ga ba shi matsayin Member of the National Institute (mni).
Certificate in Leadership, Kings College London, a shekarar 2018.
Advanced Management Development and Good Governance Certificate, Thames Valley University, London, a shekarar 2007.
Certificate in Management Skills in Rural Development, University of Reading, United Kingdom, a shekarar 1993.
Certificate in Project Management, Planning, Implementation and Control, Agricultural and Rural Management Training Institute (ARMTI), Ilorin, a shekarar 1993.
Ya kuma halarci Taron Kasa da Kasa na 6 kan Talauci da Kariya ga Al’umma (Social Protection) da aka gudanar a Bangkok, Thailand, a shekarar 2013.
Rubuce-rubuce da bincike
Alhaji Baba Mallam Wali ya rubuta ayyuka daban-daban, wadanda wasu aka wallafa wasu kuma ba a wallafa su ba.
Daga cikin rubuce-rubucensa akwai wata takarda mai taken “General Integrated Rural Development: The North East Arid Zone Development Programme”, wadda ya gabatar a wani taron karawa juna sani kan bunkasa tattalin arziki a Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda NIPSS, Kuru ta shirya a shekarar 1997.
Ya kuma rubuta wata takarda mai taken “A Strategy for Monitoring, Forecasting, Early Warning System and Integrated Pest Management in the Sudano-Sahelian Zone”. An gabatar da wannan aiki a cikin kundin wani taron karawa juna sani kan sauyin yanayi, albarkatun ruwa da bunkasar aikin noma, musamman kan matsalolin samar da abinci a yankin Afirka kudu da Sahara. An shirya taron ne a karkashin STARTAVCRP/ORSTOM/SCOWAR a shekarar 1997, a Cotonou, Jamhuriyar Benin, karkashin editan Hassan Virji da wasu.
Haka kuma, ya gabatar da muhimmiyar takarda (lead paper) a jerin laccocin farko da Jami’ar Jihar Yobe ta shirya, mai taken “Environmental Problems in Yobe State: Challenges and Opportunities” — wato Matsalolin Muhalli a Jihar Yobe: Kalubale da Damar Ci Gaba, a shekarar 2022.
Tarihin aikinsa
Alhaji Baba Mallam Wali ya fara aikin gwamnati a shekarar 1982 a Chad Basin Development Authority (CBDA) a matsayin Planning Officer (Jami’in Tsare-tsare), bayan ya kammala hidimar kasa ta NYSC a makarantu biyu, wato Abaji da Kwali Secondary Schools, a Babban Birnin Tarayya (FCT), a shekarar 1981/1982.
A lokacin da yake aiki a CBDA, ya rike mukamai daban-daban, ciki har da Shugaban Sashen Tsare-tsare (Head of Planning Division) na South Chad Irrigation Project, New Marte.
Daga shekarar 1987 zuwa 1989, ya yi aiki a matsayin Social Mobilisation Officer (Jami’in Wayar da Kan Jama’a) na Karamar Hukumar Nguru, karkashin Directorate for Social Mobilisation (MAMSER).
A
shekarar 1989, ya koma aikin gwamnatin Jihar Borno a matsayin Principal Personnel Officer, inda ya rike mukamai daban-daban, ciki har da Principal Secretary ga Military Administrator a shekarar 1990.
A watan Nuwamba 1990, an tura shi aiki zuwa North East Arid Zone Development Programme (NEAZDP), wani shirin bunkasa yankunan karkara da gwamnatin tarayya, Tarayyar Turai, da gwamnatocin Borno da Yobe s**a dauki nauyinsa.
A cikin NEAZDP, ya samu karin girma har ya zama Programme Manager (Manajan Shiri) daga shekarar 1996 zuwa 1999.
Aikin NAPEP da gwamnatin Jihar Yobe
A shekarar 2000, tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya nada shi a matsayin Coordinator na farko na NAPEP a Jihar Yobe, wato National Poverty Eradication Programme (Shirin Kawar da Talauci na Kasa). Ya yi wannan aiki na tsawon shekaru uku.
Bayan kammala wa’adinsa a NAPEP, ya koma gwamnatin Jihar Yobe, inda ya rike mukamin Director a ma’aikatu daban-daban.
A shekarar 2007, an nada shi Permanent Secretary, inda ya yi aiki a:
Ma’aikatar Matasa da Wasanni;
Ma’aikatar Sufuri da Makamashi;
Ma’aikatar Muhalli; da
Sashen Administration and General Services na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha.
Mukaminsa na Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe
A ranar 2 ga Yuni, 2015, Mai Girma tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji (Dr.) Ibrahim Gaidam FCNA, FCPA, ya nada shi a matsayin Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe (Acting Secretary to the State Government).
Daga baya, a ranar 13 ga Yuli, 2015, aka tabbatar da shi a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe (SSG), mukamin da ya rike har zuwa 29 ga Mayu, 2019.
Daga ranar 29 ga Mayu, 2019 zuwa 30 ga Disamba, 2019, Mai Girma Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni CON, ya sake nada shi a matsayin Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jiha (Acting SSG).
A ranar 30 ga Disamba, 2019, aka nada shi a matsayin cikakken Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe (Substantive SSG), mukamin da ya ci gaba da rike wa har zuwa karshen wa’adin farko na gwamnatin Mai Mala Buni a ranar 29 ga Mayu, 2023.
B
ayan nasarar da Mai Girma Hon. Mai Mala Buni ya samu a zaben shekarar 2023, ya sake nada Baba Mallam Wali, mni, a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, mukamin da yake rike da shi har zuwa yanzu.
Tarihi na musamman
Baba Mallam Wali, mni, yana da wani muhimmin tarihi na kasancewa cikin wadanda aka nada kuma aka rantsar da su a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe (SSG) na wa’adi uku a jere, karkashin gwamnonin Jihar Yobe guda biyu.
Su ne:
1. His Excellency Alhaji Ibrahim Gaidam FCNA — wanda a yanzu yake rike da mukamin Ministan Harkokin ‘Yan Sanda na Tarayyar Najeriya.
2. His Excellency Hon. Mai Mala Buni Gwamnan Jihar Yobe na yanzu.
Ya fara rike wannan babban mukami tun daga 2015 zuwa yanzu, abin da ya sanya tarihinsa na aiki a matsayin SSG ya kasance na tsawon shekaru masu yawa a jere.
A yanzu shine dan takaran kujeran Gwamnan jihat Yobe a karkashin jam'iyyar APC.