15/05/2026
ADALCI, GASKIYA DA BAWA KOWA DAMA SHI NE TUBALIN DIMOKURADIYYA!
Duk irin qauna, goyon baya da karamci da al’ummar Daura, Sandamu da Mai’adua suke nunawa ga Yusuf M. Buhari bai sa ya nuna son kai ko ya hana sauran masu buri damar su ba. Wannan ya kara tabbatar da cewa shi mutum ne mai gaskiya, amana da kishin adalci.
Duk da yadda jama’a suke masa kallon wanda ya dace, cikin nutsuwa da kwarewa ya bayyana cewa tunda akwai sauran ‘yan takara da suke son tsayawa takara, to a ba kowa dama a gudanar da primary election cikin adalci da gaskiya domin jama’a su zabi wanda suke so ba tare da danniya ko fifiko ba.
Wannan dabi’a ta nuna cewa siyasa ba fada ba ce, ba kuma danniya ba ce, illa hidima ce da mutunta ra’ayin jama’a. Hakika Yusuf M. Buhari ya nuna cikakken misali na shugabanci nagari, tawali’u da biyayya ga tsarin dimokuradiyya.
Muna kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC a Daura, Sandamu da Mai’adua Federal Constituency da su fito kwansu da kwarkwatansu domin gudanar da zaben fidda gwani cikin zaman lafiya, hadin kai da kishin jam’iyya. Nasara tana tare da masu gaskiya da niyya mai kyau.
Allah Ya bada nasara ga Yusuf M. Buhari, Ya sanya alkhairi a cikin wannan tafiya, Ya hada kan al’umma, Ya kuma tabbatar da nasarar da zata amfani jama’ar wannan yanki baki daya. Ameen.
YmbReporters ✍️