27/08/2026
HON. LAWAL RUFA’I SAFANA YA HALARCI ƘADDAMAR DA SHIRIN KT1T
Mai Ba Gwamnan Jihar Katsina Shawara kan Ayyukan Ƙananan Hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya halarci bikin ƙaddamar da Kwamitocin Dasa Bishiyoyi Miliyan 11 na Shirin Katsina One-Person-One-Tree (KT1T), wanda Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., ya ƙaddamar a ranar Alhamis, 27 ga Agusta, 2026, a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina. Shirin na da nufin shuka bishiya ɗaya ga kowane mutum a faɗin jihar, tare da dasa bishiyoyi miliyan 11 domin kare muhalli da yaƙi da illolin sauyin yanayi.
Halartar Hon. Safana na da muhimmiyar rawa musamman duba da cewa shirin zai gudana ne a Ƙananan Hukumomi 34 da Mazaɓu 361 na jihar. A matsayinsa na Mai Ba Gwamna Shawara kan Ayyukan Ƙananan Hukumomi, zai kasance cikin masu ƙarfafa haɗin guiwa tsakanin gwamnatin jiha da Ƙananan Hukumomi domin tabbatar da cewa an aiwatar da shirin yadda ya kamata a matakin al’umma. Tsarin shirin ya tanadi cewa kowane shugaban Ƙaramar Hukuma zai jagoranci shirin a Ƙaramar Hukumarsa, yayin da kowane Kansila zai jagoranci shirin a Mazaɓar sa.
Shirin KT1T na daga cikin manufofin gwamnatin Gwamna Radda na “Building Your Future (BYF)”, kuma zai taimaka wajen yaƙi da kwararowar hamada da zaizayar ƙasa, bunƙasa noma da ƙarfafa al’umma wajen kare muhalli. Gwamna Radda ya jaddada cewa nasarar shirin ba za ta ta’allaka kawai kan yawan bishiyoyin da aka dasa ba, sai dai kan waɗanda s**a rayu, s**a girma kuma s**a samar da tasiri mai ɗorewa. An kuma sanar da cewa za a fara aiwatar da shirin a hukumance a faɗin jihar daga ranar 10 ga Satumba, 2026.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki, ciki har da Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Sauyin Yanayi, Farfesa Al’amin Muhammad; Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautun Gargajiya, Hon. Bishir Tanimu; Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Alh. Abdulkadir Mamman Nasir; shugabannin Ƙananan Hukumomi, Kansiloli da sauran mambobin kwamitocin shirin.
August 27, 2026.