02/02/2022
GODIYA TA MUSAMMAN
A madadin wannan ƙungiya, ina so in Mika godiya ta musamman ga gwamnan jihar Kebbi da soyayyar da ya nuna ma kasar Sakaba a mulkin sa tun daga 2015 har zuwa 2022 da muke ciki.
Ayukka na alkhairi daban daban sun shigo kasar mu, tun daga jajircewa wajen zabe muna shuwagabanni masu kishin kasa ba kishin aljihun su ba zuwa ayukka da haskaka gari. Anyi muna t**i a cikin gari mai inganci da hanyar ruwa, an gyara makarantu, an ba yan majalisu kudi sun gyara masallatai da kuma tallafawa da abubuwa da yawa masu k**a da haka.
Babban aiki da ya sa dole duk mai son Sakaba ya ajiye makami ya bi gwamna shi ne hanya da ake yi daga Dirin daji zuwa Dankolo wanda duk mai hankali ya san in ba mai son ka ba, ba wanda zai yi irin wannan aiki a kasar da ba tashi ba sai in ya cika adili.
Dun haka muna mika godiyar mu kuma muna tabbatar da cewa zamu yi iya kokarin mu don mu yi mai biyayya. Allah ya taimake mu kuma ya taimaki kasar Sakaba. Amin
Kebbi State Government of Nigeria