22/08/2026
DUBBAN AL’UMMA SUN HALARCI BIKIN RUFE GASAR HON. BARRISTER JAMILA UMAR GURAMA UNDER-21
An gudanar da bikin rufe Hon. Barrister Jamila Umar Gurama Under-21 Football Competition – First Edition cikin yanayi na musamman, cike da farin ciki, zumunci da armashi.
Wasan ƙarshe ya gudana tsakanin Kelly Feeders da No Case Academy, inda Kelly Feeders ta yi nasara da ci 1–0, ta lashe babban wasan ƙarshe.
Muna taya Kelly Feeders murnar wannan gagarumar nasara, tare da yabawa 'yan wasa, masu horaswa da shugabannin ƙungiyar bisa jajircewarsu.
Haka kuma, muna miƙa saƙon jaje da ƙarfafa gwiwa ga No Case Academy bisa rashin samun nasara. Wannan ba ƙarshen tafiya ba ne; nasara da rashin nasara suna daga cikin rayuwar wasanni. Muna ƙarfafa su da su ɗauki darasin wannan wasa, su ƙara himma da mayar da hankali wajen shirye-shiryen wasanni na gaba.
Dubban al’umma da s**a halarci wannan wasa sun nuna irin farin cikin da suke da shi da kuma muhimmancin irin wannan shiri wajen bunƙasa harkokin matasa.
Wannan gasar ta kuma nuna ƙudurin Barrister Jamila Umar Gurama na tallafa wa matasa, gano hazaka da ƙarfafa musu gwiwa. A ganinta, saka jari a matasa shi ne saka jari a makomar al’umma.
Ta hanyar irin waɗannan shirye-shirye, Barrister Jamila ta nuna cewa hidimar al’umma ba ta tsaya ga magana ba; tana buƙatar aiki, kusanci da jama’a da ɗaukar matakin da zai amfani al’umma.
Muna kuma ƙara neman goyon bayan al’ummar Dukku Ta Kudu domin ba Barrister Jamila damar ci gaba da wannan hangen nesa na tallafawa matasa, ilimi, wasanni da sauran harkokin ci gaban al’umma.
Muna taya Kelly Feeders murna, muna ƙarfafa No Case Academy, kuma muna godiya ga dukkan waɗanda s**a taimaka wajen ganin wannan gasa ta zama tarihi.
Barrister Jamila Umar Gurama — Wakilci Mai Kusanci, Hidima Mai Ma’ana.
SDP — Farin Doki Cikin Tsira.
✍️ Tsarawa da Rubutawa:
Abdulhakim Jibril Ahmad Dukku
(Bin Maryam, Colina Dukku)
Barrister Jamila Umar Gurama Media Team