22/07/2026
Kimanin Hanyoyi guda 20 Gwamna Radda Ya Kaddamar da Fara Aikin su a Cikin Garin Malumfashi wanda zasu laƙume fiye da Naira Biliyan 10.
A ranar Talata 21/7/2026, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya za'a harsashen fara aikin gina hanyoyin guda (20) masu tsawan kilo mita 10.7 a cikin garin Malumfashi,a wani bangare na gwamnatinsa na inganta garuruwa a fadin jihar Katsina.
Kamfanin Mothercat Limited ne zai gudanar da aikin, yayin da Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Katsina za ta sa ido domin tabbatar da inganci da bin ƙa’idojin aikin.
Da yake gabatar da jawabin shi Gwamna Radda ya bayyana cewa aikin ya kasance amsa ga wata muhimmiyar buƙata da al’ummar Malumfashi s**a daɗe suna nema ta inganta hanyoyin sufuri a yankin.
Gwamnan yaci gaba da cewa" Samar da ingantattun hanyoyi zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da jigilar kayayyaki, bunƙasa harkokin noma da kasuwanci, inganta tsaro, tare da ƙara haɓaka ayyukan tattalin arziki a cikin garin Bakori da kewaye.
Gwamnan ya bayyana cewa aikin wani ɓangare ne na babban shirin gwamnatinsa na sauya fasalin al’umma ta hanyar zuba jari mai ma’ana a fannonin samar da hanyoyi, ilimi, kiwon lafiya, noma, samar da ruwa, tsaro da bunƙasa tattalin arziki.
Ya jaddada cewa ci gaba dole ne ya shafi dukkan sassan Jihar Katsina, yana mai bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Katsina, Injiniya Dakta Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa aikin na nuna ƙudirin Gwamna Radda na samar da abubuwan more rayuwa da suke amfanar jama’a.
Kwamishina yace" an zaɓi hanyoyin ne domin magance matsalolin zirga-zirga da al’ummar Bakori ke fuskanta, inda ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta tabbatar da cikakken sa ido domin ganin an gudanar da aikin yadda ya kamata, bisa ƙa’idojin da aka tsara da kuma kammala shi cikin lokaci.
Engr Sani Magaji ya ƙara da cewa haɗa fitilun hasken rana a cikin aikin na nuna yadda gwamnatin jihar ke mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa masu ɗorewa, waɗanda za su ƙara tsaro tare da tallafa wa harkokin kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arziki musamman da dare.
A nashi jawabin, wakilin kamfanin Mothercat Limited, kamfanin da ke gudanar da aikin, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Jihar Katsina bisa wannan dama, tare da yin alƙawarin kammala aikin cikin inganci da bin ƙa’idojin da aka amince da su a cikin lokacin da aka tsara.
Ya tabbatar da cewa kamfanin zai samar da ƙwararrun ma’aikata, kayan aiki da dukkan abubuwan da ake buƙata domin ganin aikin ya yi nasara, tare da yin aiki kafada da kafada da ma’aikatar da kuma al’ummar yankin.
Da yake magana a madadin al’ummar Malumfashi, Shugaban Karamar Hukumar Malumfashi Hon Muntari City, ya yaba wa Gwamna Radda bisa amincewa da wannan aiki, yana mai bayyana shi a matsayin gagarumar gudummawa da za ta inganta harkokin sufuri, kasuwanci da walwalar jama’ar yankin.
Ya kuma tabbatar da haɗin kan al’umma wajen ba da goyon baya ga kamfanin da kuma kare wannan muhimmin aikin bayan kammalawa.
Shima Sanatan Katsina ta Kudu, Sanata Muntari Dandutse, ya yabawa gwamnan bisa wannan gagarumin aiki tare da tabbatar da goyon bayan al’ummar yankin don samun nasarar aikin.
Mutane da dama s**a tofa albarkacin bakinsu daga ciki akwai Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi Mai Shari'a Sadiq Abdullahi Majiya, shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi Hon. Muntari City.
Taran ya samu halartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura, Sanatan da ke wakiltar Katsina ta Kudu (Funtua), Sanata Muntari Dandutse, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dakta Bishir Gambo Saulawa,
Sauran sun haɗa da tsohon sanatan shiyyar Funtua Sanata Bello Mandiya, Kwamishina ta harkokin mata Hon. A'isha Aminu Malumfashi, shugabannin ƙananan hukumomi, ‘yan majalisu, sarakunan gargajiya, mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar, manyan jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, wakilan al’umma; da shugabanni da ma’aikatan kamfanin Mothercat Limited.