29/05/2026
GWAMNA BUNI YA GINA CIBIYOYIN KIWON LAFIYA 148 DA HANYOYI SAMA DA KILOMITA 500 CIKIN SHEKARU BAKWAI – MUKADDASHIN SAKATAREN GWAMNATIN JIHAR YOBE
Gwamnatin Jihar Yobe ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta samu gagarumar nasara a bangarorin kiwon lafiya, gine-ginen hanyoyi, tsaro, ilimi da bunkasa tattalin arziki cikin shekaru bakwai da s**a gabata, inda ta gina cibiyoyin kiwon lafiya guda 148 tare da hanyoyi sama da kilomita 500 a sassan jihar.
Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dakta Mohammed Goje (FRSPH), ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ofishin SSG da ke Damaturu domin bikin cika shekaru bakwai na gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni.
Dakta Goje ya bayyana wadannan nasarori a matsayin hujja karara da ke nuna kudurin gwamnatin wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar zuba jari a muhimman bangarori da kuma aiwatar da manufofin da s**a shafi jama’a kai tsaye.
A cewarsa, tun bayan hawan gwamnatin a shekarar 2019, gwamnatin Gwamna Buni ta mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya, karfafa cibiyoyin gwamnati, bunkasa ilimin jama’a, fadada ayyukan more rayuwa da kuma farfado da tattalin arziki.
Ya kara da cewa gwamnatin ta kammala cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 143 daga cikin cibiyoyi 178 da aka tsara a dukkan mazabun siyasar jihar. Haka kuma ta inganta manyan asibitoci guda biyar zuwa matakin kwararrun asibitoci (Specialist Hospitals), tare da kafa cibiyoyin kula da uwa da jariri na zamani domin kara inganta harkokin lafiya.
Mukaddashin SSG ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta gina tare da gyara hanyoyi sama da kilomita 500 a fadin jihar Yobe, ciki har da hanyoyin cikin birane da na hada al’ummomi, domin saukaka zirga-zirga, kasuwanci, harkokin noma da kuma inganta alakar yankunan karkara.
Daga cikin manyan ayyukan da ya lissafo akwai aikin gada ta sama da ta karkashin kasa da ake ginawa a Damaturu, hanyar Damaturu zuwa Kalallawa, hanyar Damaturu zuwa Gambir, hanyar Waziri Ibrahim Bypass da sauran muhimman hanyoyi da ake aiwatarwa a yankunan sanatoci uku na jihar.
Dakta Goje ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a bangarorin tsaro, ilimi, noma, gidaje, samar da ruwa da wutar lantarki a karkara, yana mai cewa gwamnatin ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya tare da hanzarta ayyukan ci gaba a fadin jihar.
Ya kara da cewa sama da dalibai 48,000 ne ke cin gajiyar shirye-shiryen tallafin karatu na gwamnatin jihar, yayin da dubban matasa da mata s**a amfana da shirye-shiryen tallafawa da karfafa tattalin arzikinsu.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Dakta Goje ya tabbatar da cewa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni za ta ci gaba da kare nasarorin da aka samu cikin shekaru bakwai da s**a gabata tare da kara gina Jihar Yobe mai ci gaba, wadata da dorewar zaman lafiya.
– Umaru Sale Bebeji