21/06/2026
Assalamu Alaikum, Cikin ikon Allah Maɗaukakin Sarki, a yau na samu damar gabatar da takardar tsayawa takara ta (INEC Nomination Form) domin neman kujerar Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai wakiltar Bade Central ga Shugaban PDP na Karamar Hukumar Bade, Alhaji Gagara, da Jagoran Matasan PDP na Jihar Yobe, Alhaji Wambai Bulama, domin neman albarka, shawarwari da addu'o'insu.
Na yi matuƙar godiya bisa kyakkyawar tarba, shawarwari da fatan alherin da s**a yi mana. Wannan mataki wata alama ce ta ƙudirin yin siyasa mai tsafta, haɗin kai da aiki domin ci gaban al'ummar Bade Central.
Da yardar Allah, za mu ci gaba da tafiya tare da jama'a, mu saurari muradunsu tare da yin aiki domin cigaban matasa, mata, manoma da daukacin al'umma.
Allah Ya sanya albarka a wannan tafiya, Ya ba mu nasara da ikon sauke amanar al'umma. Amin.
Muhammad Bako Tagwai (Bamba)
Mai neman kujerar Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai wakiltar Bade Central (PDP)