23/03/2022
Hon. Kabiru Ahmadu (YARON KIRKI GIWA) kenan a lokacin daya gana da shuwagabannin wards guda shida dake Giwa Ta Yamma, k**ar haka:
1. Kadage Ward
2. Kidandan Ward
3. Galadimawa Ward
4. Yakawada Ward
5. Idasu Ward
6. Panhauya Ward
A taron daya gudana, Yaron Kirki Giwa, ya kaddamar da kansa a wajen waɗannan shuwagabanni, ya kuma roki da su bashi goyon baya da hadin kai domin dawo da martaba, zaman lafiya a Giwa Ta Yamma. A cikin Jawabin sa, ya faɗi manufofin sa k**ar haka;
1. Samar da Tsaro ta hanyar aiki hannu-da-hannu da gwamnatin jaha da kuma ta tarayya.
2. Inganta Ilimi da bayar da tallafi ga marasa karfi a yankin Giwa ta Yamma.
3. Bada tallafi ga manoma k**a a aljihunsa da kuma jawo tallafin noma na jaha da tarayya zuwa Giwa ta Yamma.
4. Samawa matasa aikin yi musamman waɗanda s**a kammala karatu.
Da sauran su.
Bayan kammala jawaban sa, chairmomin waɗannan wards sunyi murna da irin karramawa da yayi musu, kuma sun nuna gamsuwar su cewa "Lallai Ya amsa sunan sa YARON KIRKI". Shuwagabannin wards sunyi alkawarin bashi goyon baya, shawarwari, da haɗin kai don kawo sauyin gwamnati a Giwa Ta Yamma dama kasar baki daya.
A karshe, YARON ƘIRKI ya miƙawa ko wani Chairman takardar kaddamar da kansa na fitowa takarar kujerar Ɗan Majalisar Giwa Ta Yamma (Giwa West Constituency).
Gobe Ta Allah Ce!
YARON KIRKI GIWA 2023 IN-SHA-ALLAH!!
Prince Muhd Kadade Suleiman Ahmed Mohammed Makarfi HON. LAWAL SAMAILA YAKAWADA SOCIAL MEDIA SUPPORT BASE Giwa Student Association (GISA) PDP YOUTHS AWARENESS OF NIGERIA KADAGE WARD(PDP) SOCIAL MEDIA GROUP, MURYAN YAN GALADIMAWA WARD IDASU WARD SOCIAL MEDIA TEAM Panhauya Panhauya Hon AMINU YA'U GIWA Lawal Adamu Usman