03/09/2026
SAƘON TA’AZIYYA
Hon. (Dr.) Aishatu Jibril Dukku (Gimbiyar Dukku), Tsohuwar Ministar Ilimi ta Tarayyar Najeriya kuma Ambassadar Renewed Hope Initiatives, Jihar Gombe, a ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, tana miƙa saƙon ta’aziyyarta ga Amb. Haruna Garba da iyalansa, bisa rasuwar ɗansa.
Hon. (Dr.) Aishatu Jibril Dukku ta bayyana matuƙar alhininta da jimaminta bisa wannan babban rashi, tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, ‘yan uwa, abokan arziki da duk waɗanda wannan rashi ya shafa.
A cewar Gimbiyar Dukku, marigayin ya kasance matashi mai hazaka, ƙwazo, tarbiyya da girmama mutane, wanda rasuwarsa ta kasance babban gibi ga iyalansa da al’umma baki ɗaya.
Ta kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya jiƙansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.
Haka nan, ta roƙi Allah Ya bai wa Amb. Haruna Garba, iyalansa da sauran ‘yan uwa haƙuri, juriya da ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi, Ya maye musu da alheri, Ya kuma kiyaye sauran ‘ya’yansu da iyalansu.
Muna addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa, Ya sanya Aljanna ce makomarsa. Amin Ya Rabbal Alamin.
KABIRU ABIDOKA HASHIDU
(Dan Lawan Hashidu)