23/08/2026
HON. ABUBAKAR HARUNA BAKO YA KAI ZIYARAR GIRMAMAWA GA MANYAN JAM'IYYAR APC DA MASU RUWA DA TSAKI A CECENIYA, FIRE SERVICE, DA LONDON MAI DAURAWA
Hon. Abubakar Haruna Bako ya kai ziyarar girmamawa ga manyan jagororin jam'iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki a unguwannin Ceceniya, Fire Service, da London Mai Daurawa da ke cikin Ward ɗin Shamaki.
Manufar wannan ziyara ita ce nuna godiyarsa ga goyon bayan da s**a bashi, da kuma ci gaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu. Haka kuma, ya yi amfani da damar wajen sauraron ra'ayoyinsu da shawarwarinsu masu ɗauke da hikima.
An karɓe shi da kyakkyawar tarba, inda dattawan s**a ba shi shawarwari masu inganci da ƙarfafa gwiwa.
Hon.Abubakar Haruna Bako ya nuna matuƙar godiyarsa ga wannan karramawa, kuma yana ɗaukan shawarwarin dattawan a matsayin shawari mai amfani da daraja a gare shi.
Daga karshe Hon. Abubakar Haruna Bako ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da kulla wannan alaƙar girmamawa, da fahimtar juna, yayin da ya nemi suyi aiki tare domin samar da zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban al'umma
Signed;
Hon. Abubakar Haruna Bako Media Team.