06/08/2026
A ranar 5 ga watan Agusta, 2026
a Arewa House da ke Kaduna, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) Dr. Prince Adewole Adebayo, ya bayyana cewa za a iya magance matsalolin rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da kalubalen tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta cikin shekaru uku idan aka zabi shugabanni masu kwarewa da gaskiya.
Yayin da yake jawabi a taron wayar da kan jama'a na Arewa kan hadin kai wajen yaki da rashin tsaro a Kaduna, Adebayo ya ce matsalolin kasar sun dade suna ci gaba ne saboda rashin shugabanci na gari, inda ya jaddada cewa tuni aka san hanyoyin magance su.
Babu wata matsala a Najeriya da shugabanci na gari da ingantaccen jagoranci ba za su iya magancewa ba cikin shekaru uku. Matsalolin a bayyane suke ga kowa. Abin da muke bukata yanzu shi ne shugabanni da ke da shirin samar da mafita.
Dan takarar na SDP ya bayyana yankin Arewa a matsayin ginshikin makomar kasar, inda ya ce ya kamata a yi amfani da yawan al'ummar yankin da kuma dumbin albarkatun kasa da yake da su wajen bunkasa tattalin arziki, maimakon kallon su a matsayin nauyi.
Arewa ita ce makomar Najeriya, makomar yankin Sahel da kuma Yammacin Afirka. Yawan al'ummarmu babban jari ne idan muna da shugabancin da ya dace wajen tafiyar da su," in ji shi. Dr. Prince Adewole Adebayo ya yi kira ga 'yan Najeriya da su daina kallon kansu a matsayin marasa karfi, inda ya tunatar da su cewa tsarin dimokuradiyya yana bai wa 'yan kasa ikon zabar shugabannin da za su iya magance matsalolinsu.