10/08/2026
DA DUMI-DUMI: Yar Sanata Natasha Mai Shekara 16 Ta Gina Gidan Marayu A Kogi Ba Tare Da Kuɗin Mahaifiyarta Ba
Daga Ayau News//Sadiya Yusuf
Nadia Zakaria, ’yar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai shekaru 16, ta gina tare da samar da kayan aiki cikakke a Gidan Marayu na Oyiza-Salem Divine da ke Okene, Jihar Kogi.
Nadia ta ce ta fara tunanin aikin ne tana da shekara 15, inda ta tara kuɗin ginin tare da taimakon iyali, abokai da sauran masu kishin al’umma. Mahaifiyarta, Sanata Natasha, ta ce ba ta ba Nadia ko sisi ba, domin ’yar tata ce ta tara kuɗin da kanta.
An mika gidan ga marayun ne a wani biki da aka gudanar a ranar Asabar.
Menene Raayinku?
LIKE // SHARE & FOLLOW ~ Ayau News