22/05/2026
FASARAR HUDUBAR MASSALACIN JUMUAH NA UMAR IBN ABDILAZIZ ALBARKAWA GUSAU, TA RANAR JUMUAH 5/12/1447.22/5/2026.
TAKENTA SHI: Layya da Abinda ta kunsa.
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda yake cewa Kuma maganarsa gaskiya ce "Jininda kuke yankawa ko Naman bashi ne yake kaiwa ga Allah ba, saidai Jin tsoron Allah dinku shi yake samunsa".
Kuma Ina shaida Babu abin bauta bisa can canta sai Allah shikadai yake ba yada abokin tarayya Wanda yake shikadai abin nuhi da bukatu, Kuma Ina shaida lallai Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam bawansa ne Kuma manzonsa ne Wanda aka Aiko da shiriya da Rahma da Bushara, Allah kayi salati da Albarka garesa da iyalansa da sahabbansa da matayensa da zuriyarsa kamar yadda kayi salati da Albarka ga Ibrahim Kai abin yabo ne Mai Girma.
Bayan haka "Hakika Allah ya bada labari Kuma Bai gusheba yana Mai Girma cewa yanka na ibada da zubarda jini da sunan Allah Bai gusheba yana abin sharantawa cikin sharioinda s**a gabata "Kowace Alumma mun Sanya mata ibadar yanka domin su ambaci sunan Allah bisa abinda ya arzurta su dashi daga Dabbobin nima abin bautarku abin bauta guda ne ku Mika wuya garesa".
Abin nuhi mun sharanta ga alummomin da s**a gabata tun zamanin Ibrahim Aminci ya tabbata garesa zuwa wadanda s**azo bayansa wasu nauo'in ibadu Kuma ya Sanya dalilin yin haka su ambaci sunan Allah Wanda dunayensa sun tsarkaka ga ibadodi abin bauta guda ne Koda abinda aka dorawa halittu ya ban banta saboda ban bantuwar zamani da mutane da wuri saboda banbantuwar maslaha, kada ku ambaci sunan Wanin Allah ga yankan ku ku tsarkake ibada garesa shikadai ta yadda Babu wata shirka da zata shigesa gaba daya.
Ibn Abi Hatim ya ruwaito cewa "Mutanen jajhiliyya suna kawo nama a daki Mai tsarki sai sahabbai s**ace mu mukahi can canta da wannan sai Allah ya saukarda "Amanda kuke yankawa ko jinin bashi ne yake zuwa ga Allah ba,saidai Jin tsoron Allah dinku shi yake kaiwa garesa".
Ita layya an sharanta muku ita domin ku ambaci Allah sadda zaku yankata domin shine Mai arzurtawa mahalicci ba abinda yake zuwa wajensa na nama ko jini, shi Allah madaukakin mawadaci ne daga duk Wanda bashi ba.
Layya ta tabbata ta Hanyoyi ukku wato maganar Annabi aikinsa da Kuma tabbatarwarsa.
Domin ya kwadaitar da yin layya Kuma yayi umurni da ita.
Ibn Maja ya ruwaito daga zaid ibn Arkam yace, nicce ya manzon Allah wagga layyar da mukeyi minene matsayinta? Sai yace sunnar babanku Ibrahim ce, sai s**ace inmunyita mi zamu samu? Sai yace Kowane gashi Allah zai Baku Lada,sai s**ace Sufi hwa? Sai yace Kowane Sufi Lada ne".
Kamar yadda Tirmizi ya ruwaito cewa "Ba Wani aiki da mutum zaiyi ranar s**a Wanda Allah yake so kamar zubarda jini,zaizo ranar Alkiyama da kahoninsa da kohwatonsa da gashinsa, Kuma jini yana zuwa wajen Allah kahin ya zuba kasa ku yita domin Allah ".
Amma aikinsa, Muslim ya ruwaito daga Aisha Allah ya yarda da ita cewa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace a kawo masa rago Mai kahoni Mai takawa cikin Baki Mai kallo cikin Baki sai akazo masa dashi domin yayi layya dashi, sai yace mata kawomin Yuka sannan yace kodamin ita saita Koda ta ga dutsi sai ya karba ya kwantarda ragon sannan ya yanka yace da sunan Allah Allah ka karbama Muhammad da alummar Muhammad sannan yayi layya dashi.
Amma tabbatarwarsa ya kasance sahabbansa suna yin layya yana gani Kuma ya tabbatarda su akan haka".
Jundub ibn Sufyan yace "Na halarci sallar layya tareda manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam lokacinda ya kare sallah da mutane sai ya Kalli ragunan duk an yanke sai yace Duk Wanda ya yanke kahin sallah to ya sake Wanda Kuma Bai yanka ba to ya yanka da sunan Allah ".
Cewa layya wajibi ce ga Wanda ya Sami iko yahi karhi domin tana cikin Alamomin Addini, Kuma domin Allah ya sharanta ta ga Wanda ba makka yake ba domin samun dai daito ga bayi cikin samun kusanci zuwa ga Allah ta hanyar sokewa cikin kowane gari, wannan yana cikin nimar Allah da rahmarsa, kamar yadda Wani Bai iya zuwa Makkah domin yanka hadaya sai aka Sanya layya duk inda mutum yake a duniya, ita tana cikin Alamomin Addinin Allah.
Wassalamu Alaikum warahmatullahi
Imamu Bashir Siraj Gusau.