03/09/2026
JARIDAR DAILY TIMES TA KARRAMA GWAMNA DAUDA LAWAL A BUKIN CIKARTA SHEKARA 100
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi lambar yabo ta Gwamna Mafi Fice daga jaridar Daily Times a yankin Arewa maso Yamma, yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar jaridar da aka gudanar a Abuja.
Gwamnan ya karɓi lambar yabon ne a yau a wajen bikin DTN@100 Times Heroes Awards, wanda jaridar Daily Times, wadda ita ce jarida mafi daɗewa a Najeriya, ta shirya domin bikin cika shekaru 100 da kafuwarta.
An karrama Gwamna Lawal ne saboda jagorancinsa, hidimar jama’a da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasa.
Lambar yabon na daga cikin shirye-shiryen bikin cika shekaru 100 na jaridar, wadda aka fara bugawa a shekarar 1926, kuma ta kasance tana rubuta tarihin ci gaban Najeriya ta fuskar siyasa, tattalin arziki, zamantakewa da al’adu tsawon ƙarni guda.
Shugaban Majalisar DTN@100 Heroes Awards, Bolaji Okusaga, ya bayyana cewa an zaɓi Gwamna Lawal ne saboda ya samu mafi yawan ƙuri’un gabatar da sunaye a yankin Arewa maso Yamma.
Ya ce:
“Bayan gudanar da cikakken tsarin gabatar da sunaye da kuma kaɗa ƙuri’a daga jama’a, ka samu mafi yawan ƙuri’u a wannan rukunin na lambar yabo.
“Daga bisani, Majalisar Times Heroes Award da sauran muhimman masu ruwa da tsaki sun tabbatar da zaɓenka, bisa la’akari da jagorancinka, hidimar jama’a da kuma gudunmawarka wajen ci gaban ƙasa,” in ji Mista Okusaga.
Gwamna Lawal ya bayyana godiyarsa ga Hukumar Daraktoci, Masu Gudanarwa da Kwamitin Shirya bikin Daily Times Nigeria @100 Celebration, da Majalisar Times Heroes Award, da kuma dukkan ‘yan Najeriya da s**a mara wa takararsa baya.
Ya bayyana cewa wannan karramawa ta nuna irin jajircewarsa wajen inganta shugabanci na gari da kuma samar da ingantaccen aikin yi wa jama’a hidima a Jihar Zamfara.
Sauran fitattun ‘yan Najeriya da aka karrama sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, da kuma tsohon Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adesina.
Jaridar ta sanar da cewa za a saka sunayen waɗanda s**a karɓi lambobin yabo na DTN@100 Times Heroes Awards cikin fitattun mutane da cibiyoyin da s**a fi taka muhimmiyar rawa, a cikin littafin Nigerian Grand Book mai shafuka 700.
“Wannan littafi zai kasance kundin tunawa na ƙasa, tare da zama tarihi na dindindin game da mutane, cibiyoyi da nasarorin da ke taka rawa wajen tsara ci gaban Najeriya.”
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya rubuta gabatarwar littafin Nigerian Grand Book.
SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
3 ga Satumba, 2026