30/09/2013
JAIZ BANK YA ZO ZAMFARA.
Watan Azumin da ya gabata, malamai a wuraren tafsir sunyi kira ga masu hali da su zabude asusun ajjiya a bankin Musulunci domin bankin ya cika bukatun da gwamnatin tarayya tayi.
A nashi haujin, gwamnan jahar Zamfara Hon Dr Abdul'aziz Yari Abubakar Shettiman Mafara kuma cigarin Gumi ya bayyana sanya zunzurutun kuddi har N1.5 Billion.
Gwamnan ya bukaci masu hannu da shuni da su gaggauta bude asusun ajiya a bankin domin gudanar da harkar kuddi wadda babu ruwa.
Shi dai wannan banki akwai shi kasashe masu yawa irinsu Birtaniya da America.