10/10/2025
Sheikh Bala Lau ya goyi bayan Sheikh Triumph, ya yi gargaɗi kan tsoma siyasa a lamarin addini.
Daga Jibwis Nigeria
Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iƙamatissunnah (JIBWIS) ta Tarayyar Najeriya, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa babu wata ƙungiya da ke tsayawa tsayin daka wajen kare martabar Manzon Allah (S.A.W) k**ar Ahlussunnah.
Babban shafin 'Jibwis Nigeria' ya ruwaito Shehin Malamin Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da Khudba a ranar Juma’a, 10 ga watan Oktoba 2025, a masallacin JIBWIS na ƙasa dake unguwar utako a birnin Abuja, inda ya ce tirka-tirkar da ke faruwa tsakanin Sheikh Lawal Abubakar Shu’aib Triumph da wasu Malaman Bid’ah a Kano darasi ne ga al’umma.
Sheikh Bala Lau ya jaddada cewa Ahlussunnah su ne masu kare gaskiya da bayyana ƙarya da ƴan Bid’ah ke jingina wa Manzon Allah (S.A.W). Yana mai cewa Da’awar Ahlussunnah tana gudana ne bisa tafarkin Musulunci, ƙarƙashin koyarwar Alƙur’ani da ingantattun Hadisan Annabi Muhammad (S.A.W). “Ahlussunnah su ne suke ƙalubalantar waɗanda ke alaƙanta wa Annabi abubuwan da addini bai zo da su ba, kuma wannan ne ke tabbatar da gaskiyarsu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa soyayya ga Manzon Allah ba ta tabbata cikin jahilci. Allah da Sahabbai ne s**a fi kowa son Annabi, kuma duk lokacin da Sahabbai s**a yi waƙa wadda ta zarce ƙa’ida, Annabi (S.A.W) da kansa yake hana su. “Dole ne mu nuna soyayya ga Manzon Allah ta hanyar bin shari’a, ba ta hanyar ɓatanci ko Bid'ah ba. Allah da Sahabbai ne s**a fi mu sanin matsayin Annabi, kuma sun fi kowa sanin yadda ake girmama shi,” in ji Sheikh Bala Lau.
Da yake tsokaci kan muhawarar da Sheikh Lawal Abubakar Shu’aib Triumph ke yi da Malaman Bid’ah a Kano, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa Sheikh Triumph yana ƙoƙarin faɗakar da al’ummar Musulmi kan yadda wasu Malaman Bid’ah ke jingina karamomi ga shehunnan su, ta hanyar danganta su da Annabi (S.A.W). Ya ƙara da cewa: “Triumph yana son mutane su gane cewa Sahabbai ba su nuna soyayya ga Annabi da jahilci ba, sai dai bisa karantarwar Alƙur’ani da Hadisai.”
Shugaban JIBWIS ɗin ya kuma yi kira ga kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Kano ta kafa da su yi adalci a binciken da suke gudanarwa kan Da’awar Sheikh Triumph da ta ƴan Bid’ah. “Idan an kira Sheikh Triumph, a tambaye shi hujjoji daga Alƙur’ani da Hadisai; idan an same su, to babu sauran jayayya. Kada gwamnati ta tsoma siyasa cikin lamuran da s**a shafi addini, domin k**a malamin Ahlussunnah saboda Da’awar Musulunci ba zai haifar da da mai ido ba,” in ji shi.
A ƙarshe, Sheikh Bala Lau ya ƙaryata furucin mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya ce k**a Abduljabbar Nasiru Kabara ra’ayin siyasa ne. Ya bayyana cewa k**a Abduljabbar haɗin kai ne tsakanin Malaman Izala, Dariƙar Tijjaniya da sauran ɓangarorin Sufaye, bisa hujjar cewa Da'awar shi ta saba da koyarwar Alƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (S.A.W). A ƙarshen Khudbar, Sheikh Bala Lau ya yi addu’ar samun haɗin kan al’ummar Musulmi da samun zaman lafiya a Najeriya da duniya baki ɗaya.
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1263658785808316&id=100064926180538&mibextid=ZbWKwL
✍️ Ibrahim Baba Suleiman
DG Social Media
Jibwis Nigeria