KAM YOUTH 2027

KAM YOUTH 2027 This movement is driven by determined youth,
And this page was created entirely for the politics of the Member representing Gusau/Tsafe,
Hon.

Kabiru Amadu Mai Palace,
to showcase:
His policies
And His developmental projects in his constituency.

AN NADA BINTA RAZAK A MATSAYIN SHUGABAR MATAN KAM YOUTH 2027 A madadin Mai Girma Chairman Muhammad Ibrahim, muna farin c...
20/08/2026

AN NADA BINTA RAZAK A MATSAYIN SHUGABAR MATAN KAM YOUTH 2027

A madadin Mai Girma Chairman Muhammad Ibrahim, muna farin cikin sanar da Binta Razak a matsayin Shugabar Matan Ƙungiyar KAM YOUTH 2027.

Wannan naɗi ya zo ne domin ƙara ƙarfafa rawar da mata ke takawa wajen tafiyar da harkokin ƙungiyar, tare da ba su damar bayar da gudummawarsu wajen cimma manufofin KAM YOUTH 2027.

Muna taya Bintu Razak murna bisa wannan babban matsayi, tare da yi mata fatan samun nasara da ikon sauke nauyin da aka ɗora mata.

Allah Ya ba ta ikon gudanar da wannan amanar yadda ya kamata, Ya sa wannan naɗi ya zama alheri ga ƙungiya da al’umma baki ɗaya.

Muna taya ki murna, Binta Razak!

KAM YOUTH 2027 — Haɗin Kai, Ƙarfafawa da Ci Gaba.

Hon Kabiru Amadu Go again 😍💪

19/08/2026

Gusau Da Tsafe!!
Sai Mai Palace 😍

DA DUMI-DUMI: Mai Martaba Yandoton Tsafe ya bayyana jin daɗinsa da irin ayyukan ci gaba da Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ...
19/08/2026

DA DUMI-DUMI: Mai Martaba Yandoton Tsafe ya bayyana jin daɗinsa da irin ayyukan ci gaba da Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ya samar, ba a Ƙaramar Hukumar Tsafe kaɗai ba, har ma a faɗin al’ummar da yake wakilta.

A cikin saƙonsa, Mai Martaba ya bayyana cewa irin waɗannan ayyukan ci gaba ne s**a sa yake alfahari da Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, yana mai jaddada muhimmancin samar da ababen more rayuwa da za su amfanar da al’umma gaba ɗaya.

Ya ce:

«“Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, tabbas ka samar da ayyukan ci gaba, ba a Tsafe kaɗai ba, har ma a faɗin al’umma. Wannan ne ya sa nake alfahari da kai. Kai ne nawa!”»

Mai Martaba ya ƙara da cewa ya fi son ɗan siyasar da yake samar da abubuwan ci gaba da za su amfani al’umma, fiye da wanda zai ɗauki kuɗi ya ba mutum, komai yawan kuɗin.

«“Na fi son wanda yake samar da abubuwan ci gaba a cikin al’umma, fiye da wanda zai ɗauki kuɗi ya ba ni, komai yawan kuɗin.”»

Wannan jawabi na nuna muhimmancin ayyukan ci gaba da tasirinsu ga al’umma, musamman wajen samar da abubuwan da za su ci gaba da amfani ga jama’a na dogon lokaci.

Rahoto: KAM YOUTH 2027

KAM YOUTH 2027 😍💪DAGA TSAFE: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA ZIYARCI AIKIN GININ CBT CENTRE A TSAFEƊan Majalisar da ke w...
19/08/2026

KAM YOUTH 2027 😍💪

DAGA TSAFE: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA ZIYARCI AIKIN GININ CBT CENTRE A TSAFE

Ɗan Majalisar da ke wakiltar Gusau/Tsafe Federal Constituency, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, ya kai ziyarar duba aikin ginin CBT Centre da ke gudana a College of Health Sciences and Technology, Tsafe.

A yayin ziyarar, Hon. Mai Palace ya duba yadda aikin ke gudana tare da bibiyar matakan da ake ɗauka domin tabbatar da cewa an gudanar da aikin yadda ya kamata.

CBT Centre ɗin zai taimaka wajen samar da ingantaccen yanayi ga ɗalibai wajen karatu da gudanar da jarabawa ta hanyar kwamfuta, tare da ƙara inganta ababen more rayuwa a fannin ilimi.

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tallafa wa harkar ilimi da bunƙasa ababen more rayuwa a mazabar Gusau/Tsafe Federal Constituency.

Allah Ya sanya albarka a aikin, Ya sa ya kammala cikin nasara, Ya kuma zama abin amfani ga ɗalibai da al’ummar Tsafe baki ɗaya.

KAM YOUTH 2027 😍💪DAGA MASARAUTAR TSAFE: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA KAI ZIYARAR GIRMAMAWA MASARAUTAR TSAFEƊan Majali...
19/08/2026

KAM YOUTH 2027 😍💪

DAGA MASARAUTAR TSAFE: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA KAI ZIYARAR GIRMAMAWA MASARAUTAR TSAFE

Ɗan Majalisar da ke wakiltar Gusau/Tsafe Federal Constituency, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, ya kai ziyarar girmamawa zuwa Masarautar Tsafe, inda ya samu kyakkyawar tarba daga Mai Martaba Sarkin Tsafe, Alh. Muhammad Mamman Bawa, MON, tare da sauran masu ruwa da tsaki na masarautar.

A yayin ziyarar, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ya gabatar da jawabi ga Mai Martaba, inda ya bayyana irin ƙoƙarin da ya yi da ayyukan ci gaba da jin ƙai da ya aiwatar a Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Ya kuma bayyana aniyarsa ta ci gaba da kawo ƙarin ayyukan ci gaba ga al’ummar Tsafe, tare da jaddada cewa idan Allah Ya ba shi damar komawa Majalisar Wakilai a karo na uku, zai ƙara mayar da hankali wajen samar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma.

A nasa ɓangaren, Mai Martaba Sarkin Tsafe, Alh. Muhammad Mamman Bawa, MON, ya nuna godiyarsa bisa wannan ziyara, tare da yi wa Hon. Kabiru Amadu Mai Palace addu’ar samun nasara da fatan Allah Ya taimake shi a dukkan al’amuransa.

Ziyarar ta gudana cikin yanayi na girmamawa, zumunci da fahimtar juna, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai wajen ci gaban al’ummar Tsafe.

Allah Ya ƙara haɗa kanmu, Ya albarkaci Masarautar Tsafe da al’ummarta, Ya kuma sanya alheri da nasara a wannan tafiya.

ALLAH Shi Zai Bamu — Mai Palace Ko Gobe!

KAM YOUTH 2027 😍💪DAGA TSAFE: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA ZIYARCI ƘUNGIYOYIN MATA A TSAFEBayan kammala wani zama da m...
19/08/2026

KAM YOUTH 2027 😍💪

DAGA TSAFE: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA ZIYARCI ƘUNGIYOYIN MATA A TSAFE

Bayan kammala wani zama da masu ruwa da tsaki a Ƙaramar Hukumar Tsafe, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ya zarce zuwa Secretariat na Ƙaramar Hukumar, inda ya gana da ƙungiyoyin mata da ke garin Tsafe.

Ganawar ta gudana ne gabanin fara wani sabon zagayen kamfen da Hon. Mai Palace zai ƙaddamar a kwanaki masu zuwa, domin ci gaba da tuntuɓar al’umma da neman goyon baya.

A yayin ganawar, ƙungiyoyin matan sun bayyana farin cikinsu da ziyarar, tare da jaddada ci gaba da ba Hon. Kabiru Amadu Mai Palace cikakken goyon baya, kamar yadda s**a saba.

Sun kuma nuna aniyarsu ta ci gaba da kasancewa tare da shi wajen tafiyar da manufofinsa na siyasa da wakilcin al’umma.

Ubangiji Allah Ya sanya alheri, Ya ba Hon. Kabiru Amadu Mai Palace nasara, Ya kuma sa tafiyar ta kasance mai amfani ga al’ummar Gusau/Tsafe da Jihar Zamfara baki ɗaya.

Mai Palace Ko Gobe — Allah Shi Zai Bamu.

KAM YOUTH 2027  😍💪Hon. Kabiru Amadu Mai Palace Ya Bai wa Masu Ruwa da Tsaki na APC a Tsafe Naira Miliyan 5, Buhunan Shin...
19/08/2026

KAM YOUTH 2027 😍💪

Hon. Kabiru Amadu Mai Palace Ya Bai wa Masu Ruwa da Tsaki na APC a Tsafe Naira Miliyan 5, Buhunan Shinkafa 50 da Buhunan Taki 100.

A yayin taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC daga dukkanin bangarorin siyasa a Tsafe, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ya tallafa wa mahalarta taron da buhunan abinci 50, Naira miliyan 5 da buhunan taki 100.

A cikin jawabinsa, Mai Palace ya bayyana irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban ilimi, jinƙai da walwalar al’umma a Tsafe, ciki har da:

Daukar nauyin ɗalibai talatin-talatin 30-30 a kowace makarantar firamare da sakandare masu zaman kansu a Tsafe, kan kuɗi Naira miliyan 8 a kowanne zango

Bada tallafin karatu ga sama da ɗalibai 800 daga Tsafe da ke jami’o’i, kwalejojin ilimi da polytechnics, wanda ke cin Naira miliyan 64 a kowace shekara.

Aikin Gina cibiyar CBT ta Naira miliyan 800.

Gina ajujuwa a makarantu da ofisoshi a Focal, Kwaren ganuwa, Kucheri, SDP Tsafe da sauran wurare.

Gina rijiyoyin burtsatse a Bilbis, Tsafe da sauran al’ummomi.

Samar da sabbin motoci ga shugabannin jam’iyya tun daga 2019 zuwa yau na Tsafe, da kuma mashuna ga dukkanin shugabannin ward da Tsafe.

Rarraba kayan abinci ga al’ummomin kowace ward a Tsafe, tare da tallafin taki da kuɗaɗe.

Samar da hasken rana (solar) a wards da cikin garin Tsafe, ciki harda hanyar college of health sciences and Technology

Katange Masallacin Idi, wanda ya yi alkawarin kammala shi kafin zaɓe.

Gabatar da koke da matsalolin al’ummar Tsafe a Majalisar Wakilai har sau tara.

Samar da gidaje ga wasu daga cikin matasa da abokanin siyasa a Tsafe da sauran ababen tallafi ga al’umma ciki harda gudunmuwa a asibitin Tsafe da sauran su

YANZU-YANZU: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA HALARCI ZAMAN TATTAUNAWAR APC STAKEHOLDERS NA TSAFEA yanzu haka, Hon. Kabir...
19/08/2026

YANZU-YANZU: HON. KABIRU AMADU MAI PALACE YA HALARCI ZAMAN TATTAUNAWAR APC STAKEHOLDERS NA TSAFE

A yanzu haka, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace yana halartar wani zaman tattaunawa na musamman tare da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC (APC Stakeholders) na Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Zaman ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin kai, fahimtar juna da tattaunawa kan makomar jam’iyyar, tare da duba hanyoyin da za su taimaka wajen ci gaban al’ummar Tsafe.

Taron ya kasance wata dama ga shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar domin musayar ra’ayoyi, sauraron juna da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.

APC Tsafe — Haɗin Kai, Fahimta da Ci Gaba.

KAM YOUTH 2027

Allah ya kiyayeka Da kiyayewar shi Allah yayi Maka Mafita Da Dukan Wanda ke Hannun Yan Ta'adda 🤲
18/08/2026

Allah ya kiyayeka Da kiyayewar shi
Allah yayi Maka Mafita Da Dukan Wanda ke Hannun Yan Ta'adda 🤲

Hon. Kabiru Amadu Mai Palace A Garin Shemori, Yayin Ziyarar Duba Aikin Ginin Masallacin Da yake Ginawa Al'ummar Wannan G...
18/08/2026

Hon. Kabiru Amadu Mai Palace A Garin Shemori, Yayin Ziyarar Duba Aikin Ginin Masallacin Da yake Ginawa Al'ummar Wannan Gari. 😍

Address

Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KAM YOUTH 2027 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share