16/05/2026
DA DUMI DUMI: Hon. Kabiru Amadu Mai Palace Ya Kai Ziyarar Godiya A Wanke, An Kuma Naɗa Shi Sarautar “Gamjin Wanke”
Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ya kai ziyarar musamman zuwa ƙasar Wanke domin nuna godiya ga al’umma bisa irin goyon baya da s**a nuna masa, duk da dage zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar Majalisar Tarayya na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya gudanarwa.
Ziyarar ta gudana ne a yau Asabar 16/05/2026, bayan sanar da dage zaɓen, inda Hon. Kabiru Amadu ya bayyana cewa bai ga dacewar zama shiru ba, sai ya je ya kai gaisuwa da godiya ga al’ummarsa waɗanda s**a nuna cikakken goyon baya tun kafin ranar zaɓen.
Rahotanni sun nuna cewa al’ummar yankin sun fito kwansu da kwarkwatansu domin tarbar sa, duk da cewa an dage zaɓen, lamarin da ya nuna irin ƙauna da amincewar da jama’a ke da ita a gare shi.
A yayin wannan ziyara, Mai Martaba Uban Doman Ƙasar Wanke ya karrama Hon. Kabiru Amadu Mai Palace da sarautar gargajiya ta “GAMJIN WANKE”, a matsayin girmamawa da yabawa ga irin gudummawar da yake bayarwa ga al’umma da ci gaban yankin.
Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ya bayyana matuƙar farin ciki da wannan karramawa, tare da gode wa masarauta da al’ummar Wanke, yana mai alƙawarin ci gaba da hidimtawa jama’a cikin gaskiya da riƙon amana.
Ziyarar ta kasance cikin yanayi na farin ciki, haɗin kai da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin jagora da al’ummarsa.
Rahoto: KAM Youths 2027