18/04/2026
ALAMOMI 5 DA SUKE NUNA CEWA MATASHI BA ZAI TAƁA YIN NASARA BA HAR ABADA.
Idan har kana son gane matashin da zai tsufa bai tsinana wa kansa komai ba a duniyar nan, kalle shi da kyau zaka ga yana da wadannan dabi'un. Ba maita ba ne, ba asiri ba ne; tsabar lalaci ne da shashanci wanda idan baka gyara ba, kai kadai zaka yi asarar rayuwarka.
Idan wannan rubutun zai baka haushi, to lallai da kai nake yi. Kuma gara in gaya maka gaskiya yau ka gyara, da ka zama abin dariyar sa'anninka a gobe:
1.Yawan Kuka Da Ɗora Laifi: Kullum kana kukan gwamnati ta ki baka aiki, ko iyayenka basu bar maka gado ba. Yi ta zama kana jiran wani ya zo ya share maka hawaye, Ka tsufa a dakin iyayenka kana cewa baka da sa'a. Matashin da baya daukar alhakin rayuwarsa ya fita neman halas, ba zai taba fitowa daga kaskanci ba.
2. Rainin Ƙaramar Sana'a: Baka da ko kudin sabulun wanka, amma idan an ce ka zo ka fara karamar sana'a ko ka koyi aikin hannu, sai ka wani nuna wai hakan zai zubar maka da Class. Wane irin 'class' gare ka idan har kana rokon kudin kati? Girman kan banza shine asalin kiran wulakanci. Yi ta zama ka ci gaba da jiran aikin ofis din da ba zai taba zuwa ba.
3.Rayuwar Ƙarya (Fake Life): Aljihunka babu ko sisi, amma kana rike da wayar da tafi karfinka don kawai ka burge mutanen da a zahiri ba sa ma lissafinka. Kana rance don ka yi gayu. Yi ta kashe kudin da baka da shi wajen siyan karyar wayewa, Ranar da asirinka ya tonu, masu yi maka dariya a yanzu, sune zasu fara taka ka a fili.
4. Zaman Majalisa Da Abokan Banza : Kana cikin majalisar da idan kun zauna tun daga safe har dare babu maganar yadda zaku yi fafutukar neman kudi ko ilimi. Hira kawai akan 'yan mata, kwallo, da zagin masu kudi. Kana ganin kun waye ko? Ku ci gaba da zama a wurin, Ranar da kuka cika shekaru 30 kowannenku zai gane cewa dukkan ku asararru ne da babu mai taimakon wani.
5.Tsoron Wahala da Son Jiki Kana son arzikin masu kudi, amma kana gudun tashi da asuba. Kana son zama babban mutum amma baka son shan zafin jajircewa a kasuwa. Idan kaga damar fita ka nemo na kanka, sai ka yi kwance kana baccin asara har rana ta take ka. Wallahi talauci irin wanda ba a taba ganinsa ba yana jiranka a gaba.
A karshen wadannan sune masu mahimmanci da ya kamata ka tabbata ka yi nesa da su tun a yau: Shaye-shaye, C**a, Rashin ibada da zina.
Idan wannan gaskiyar ta harzuka ka, to ka yi fushi ka tashi ka nemi mafita, Fushin namiji a kasuwa ake ganin sa ta hanyar zage damtse, ba wai ka tsani wanda ya gaya maka gaskiya ba. Duniya bata tausaya wa rago.
Allah Ya bamu ikon tsare makomarmu daga rudin duniya.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️