16/09/2020
JADAWALIN WASU CIKIN AIYUKA
DA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YA AIWATAR DAGA SHEKARA ALIF DUBU BIYU DA SHA BIYAR (2015) ZUWA ALIF DUBU BIYU DA ASHIRIN (2020).
A BANGAREN ILMI SHUGABA BUHARI YA CIMMA NASARORI KAMAR HAKA...
1)- Gina Jami'ar abubuwa da s**a Shafi Teku, (Maritime) a jihar Delta dake Shiyar kudu maso kudancin Najeria.
2)- Gina Jami'ar Sojin kasa (Army University) dake Garin Biu, jihar Borno shiyar Arewa maso Gabas.
3)- Gina Jami'a ta Harkokin Noma (Agriculture) dake Garin Zuru, jihar Kebbi shiyar Arewa maso Yamma.
4)- Kafa Tubalin Gina Jami'ar Sufuri a Garin Daura jihar Katsina, shiyar Arewa maso Kudu.
5)- Samar da kudade Naira Biliyan Dari Biyu (200 billon) ga Jami'oin dake kasar nan ta hanyar Hukumar Asusun Ilmin Mai Zurfi (TETFUND).
6)- Kafa Tubalin Gina Jami'a ta Sojin Sama a Garin Tafawa Balewa dake Jihar Bauchi Shiyar Arewa maso Gabas.
7)- Kafa Tubalin Samar da Sabbin Kolejojin Ilmi guda Shida (6) a Jihohi kamar haka;
A) Bauchi
B) Benue
C) Ebonyi
D) Osun
E) Sokoto
F) Edo
G) Da kafa Kwalejin Kimiyya da Safaha a Garin Daura jihar Katsina.
A BANGAREN KIWON LAFIYA SHUGABA BUHARI YAYI NASARA SAMAR DA ABUBUWA KAMAR HAKA;.
1)G- Babban Asibitin Jinya na Sojin Sama a Garin Daura Jihar Katsina.
2)- Babbn Asibin Sojin Sama a Garin Bauchi, dake Jihar Bauchi.
3)- Asibitin Mata da Kananan Yara dake Daura jihar Katsina.
4)- Gina Asibitin Soji dake Garin Kaduna jihar Kaduna.
5)- Gina Cibiyar Kula da masu dauke da Cutar Daji (Cancer) a Birnin Tarayya Abuja.
6)- Gina Cibiyar Kula da masu Dauke da cutar Daji (Cancer) a Babbar Jami'ar koyar wa ta Gwamnatin Tarayya dake Lagos. Jihar Lagos.
SAMAR DA KUDADEN TALLAFI GA JIHOHI.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samar da Tallafin kudade wa Gwamnonin Jihohi 27 daya kai Kimanin Biliyoyin Daloli don Cire su cikin Sananin Rashin kudi.
MANYA AIYUKAN GADOJI DA SHUGABA BUHARI YAKE AIWATAR WA.
1)- Babbar Gadar nan data Hada jihohin Delta da Anambra (Second Niger Bridge)
2)- Aikin Babbar Gadar nan ta Kogin Benue (Second Benue Brid