Office of the Chairman, Jama'are Local Government

Office of the Chairman, Jama'are Local Government Political Awareness

06/01/2026

SANARWAR DAGA TEBURIN SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR JAMA’ARE HON. INUWA ABDULLAHI MOISHA (BARADEN JAMA’ARE)

Al’ummar Karamar Hukumar Jama’are sun yi Allah wadai da zarge-zargen da ake yi na danganta Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Bauchi), da ta’addanci, tare da bayyana cewa irin waɗannan zarge-zarge ƙarya ne marasa tushe kuma an ƙirƙire su ne domin ɓata suna da hana cigaban jihar Bauchi.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Karamar Hukumar Jama’are, Hon. Inuwa Abdullahi Moisha (Baraden Jama’are) ya fitar a madadin al’ummar Karamar Hukumar Jama’are, inda ya jaddada cewa al’ummar yankin suna goyon bayan Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed dari bisa dari a ƙoƙarinsa na gina sabuwar Jihar Bauchi da inganta rayuwar al’umma.

Hon. Inuwa Abdullahi Moisha ya bayyana cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed mutum ne mai kishin zaman lafiya, hadin kai da cigaba, wanda yake jajircewa wajen samar da tsaro, ilimi, lafiya da bunƙasa tattalin arziki a faɗin jihar Bauchi.

Ya ƙara da cewa al’ummar Jama’are ba za su lamunci duk wani yunkuri na ɓata suna ko rashin gaskiya ba, tare da yin kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani labari ko zargi da ke neman tayar da hankula ko rarraba kan al’umma.

A ƙarshe, al’ummar Karamar Hukumar Jama’are sun tabbatar da cewa za su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen mara wa gwamnan baya, tare da addu’ar Allah ya ba shi ikon ci gaba da jagoranci nagari domin cigaban Jihar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya.

Sa Hannu:-
Mohammed Adamu
Babban Sakatare Na Musamman (PPS)
Ga Shugaban Karamar Hukumar Jama’are.

Address

Jama'are

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Office of the Chairman, Jama'are Local Government posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share