29/09/2026
🇨🇳 SHIN KUN SAN SHEIKH IBRAHIM NIASS YA GANA DA MANYAN JAMI’AN CHINA A 1963?
Akwai wani tarihi mai ban sha'awa game da ziyarar Sheikh Ibrahim Niass zuwa ƙasar China a shekarar 1963, wanda wasu mutane ba su sani ba.
📜 Hujjar People’s Daily ta China
A ranar 22 Oktoba 1963, Sheikh Ibrahim Niass ya isa Beijing tare da wasu daga cikin tawagarsa, bisa gayyatar China Islamic Association.
A ranar 28 Oktoba 1963, ya gana kai tsaye da:
🇨🇳 Zhou Enlai (周恩来) — Firayim Ministan China a lokacin.
Rahoton People’s Daily na ranar 29 Oktoba 1963 ya tabbatar da cewa Zhou Enlai ya karɓi Sheikh Ibrahim Niass da tawagarsa a Zhongnanhai, inda s**a yi tattaunawa cikin yanayin abota.
👥 Waɗanne jami'ai suke wurin?
Rahoton China ya ambaci waɗannan mutane a matsayin waɗanda suke wurin ganawar:
• Zhou Enlai (周恩来) — Firayim Minista
• Burhan Shahidi (包尔汉) — Shugaban China Islamic Association
• Zhang Jie (张杰) — Mataimakin shugaban China Islamic Association
• Liu Pinyi (刘品一) — Mataimakin shugaban China Islamic Association
• Zhang Tiesheng (张铁生) — Mataimakin shugaban Chinese-African People’s Friendship Association
📅 Kundin ayyukan Zhou Enlai na 1963 ya ƙara ba da takamaiman lokaci da wurin ganawar:
28 Oktoba 1963 — 2:25 na rana — Xihua Hall, Zhongnanhai, Beijing.
🕌 ME YA SA ZIYARAR TAKE DA MUHIMMANCIN GASKE?
A lokacin ziyarar, Sheikh Ibrahim ya gana da shugabannin China da kuma shugabannin Musulman China. Ya ziyarci masallatai, gidajen tarihi da Great Hall of the People.
A cikin bayanan da aka wallafa game da liyafar tasa, an bayyana batutuwan da s**a shafi zumuncin Afirka da China, yaƙi da mulkin mallaka, matsayin China a Majalisar Ɗinkin Duniya, da batun Taiwan.
Bayan dawowarsa, Sheikh Ibrahim ya kuma bayyana cewa ya gana da shugabannin China, Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, kuma ya yaba da yadda Musulman China suke gudanar da ayyukan addininsu.
⚠️ MUHIMMIN GARGADI:
Akwai labarin cewa an ba Sheikh Ibrahim damar zuwa Shanghai domin ganawa da Mao Zedong, amma har yanzu ban s