19/06/2026
Almajiri ɗan shekaru 8 ya ji mummunan rauni bayan da ƙarfen hana manyan motoci wucewa ya fado masa a Kano
Wani Almajiri mai suna Mas’udu, mai kimanin shekaru 8 ya samu mummunan rauni a kafa bayan da ƙarfen da hukumar KAROTA ke sanya wa a tituna don hana manyan motoci wucewa ya fado masa a jihar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa lamarin ya faru a yau Juma'a da misalin ƙarfe 12 na rana a titin Dan Hausa, hanyar kasuwar Farm Centre, bayan da wani direban mota kirar kanta, ya yi lodin duro-duro kuma ya cusa kan motar don ƙoƙarin wucewa ta kasan ƙarfen.
A cewa shaidun gani da ido, bayan direban ya samu nasarar wucewa, sai saman motar ya daki ƙarfen inda ya fado ƙasa lokacin da yaron da abin ya shafa ya zo wucewa sai ya sauka a kafar sa.
Wakilin mu da ke gurin daidai lokacin da hadarin ya faru ya lura cewa al'ummar da kenqajwntaun shiga firgici da alhini, inda ma'aikatan KAROTA da ke wajen da sauran jama'a aka yi kokarin dauke yaron tare da kai shi asibiti.
Da ya ke Zamfara da wakiln mu, wani almajiri da ke tare da yaron lokacin da lamarin ya faru ya ce a makarantar Malam Amadu a unguwar Tsamiya Babba da ke Hotoro a jihar Kano.
Wakilin Daily Nigerian Hausa ya lura cewa bayan da ƙarfen ya fado, ya datse saman kafar yaron har ana ganin kashin, inda ya kara da cewa kasusuwan kafar duk sun Karaye, abun ba kyawun gani.
Wakilin mu ya ƙara da cewa tuni dai jami'an yansanda da na KAROTA da direban motar s**a garzaya asibiti da yaron cikin mawuyacin hali.