07/05/2026
GANI YA KORI JI: Matasa Sun Samu Dama, Godiya ga Hon. Aminu Adam!
A Kawo Constituency, matasa sun fara ganin canji mai ma’ana! Hon. Aminu Adam, ɗan takarar majalisar jihar Kaduna, ya nuna jajircewa wajen samar da aikin yi, inda yanzu haka matasa 30 s**a yi passing out a Federal Fores Guard sanadinsa. Wannan aikin ya nuna yadda Hon. Aminu Adam ke ɗaukar bukatun al’umma da muhimmanci, musamman matasa.
Ba wai kawai zaben kujerar majalisa ba ne wannan, zaben shugaba mai hangen nesa wanda ke ganin matasa ginshiƙi na ci gaban al’umma. Tare da irin wannan jagoranci, matasa a Kawo suna samun damar shiga harkokin gwamnati, samun ilimi, da kuma tallafi a rayuwarsu.
Hon. Aminu Adam ya tabbatar da cewa siyasa a Kawo ba kawai kujerar kai tsaye ba ce, aa hanyar kawo canji mai ɗorewa ga al’umma ce.
Kawo Constituency, lokaci yayi da za mu tashi mu zabi shugaba mai aiki, wanda zai kawo wa Kawo Constituency ci gaba ta fannoni daban-daban musamman aikinyi ga mata da matasa.
Mu yi Hon Aminu Adam da farar zuciya.
Muneer Yusuf Assalafy
DG Media
Monye Media Team
07/05/2026