Taskar Hausa

Taskar Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Taskar Hausa, Badarawa main Road, Kaduna.

24/08/2026

Tallafin Man Fetur: Wasu ’Yan Najeriya Sun Nuna Goyon Bayan Atiku

A kafafen sada zumunta ma an samu ra’ayoyi daban-daban. Wasu daga cikin masu goyon bayan shirin sun ce idan gwamnati za ta yi tallafin ne ga samar da man fetur a cikin gida,

24/08/2026

Wata mata tana zargin an hanata gidan da ta saya a kawo kaduna

Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester United tayi rashin nasara a hannun Hull City a gasar ...
22/08/2026

Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester United tayi rashin nasara a hannun Hull City a gasar Premier League a duk tsawan haduwar su

Haka kuma, wannan ne karo na farko da Manchester United ta yi rashin nasara a wasan farko na kakar Premier League a hannun wata sabuwar ƙungiyar da ta d**o zuwa matakin gasar Premier League. 😬

22/08/2026

Sako na musamman daga kungiyar Relax Tinubu is Fixing Nigeria tare da City Boy Movement.

Ku bayyana mana ra’ayinku.

22/08/2026

⚽🔥 HIGHLIGHTS | QUEENS PLANET FC VS FLASH FOOTBALL

Queens Planet FC ta fafata da Flash Football a gasar NLO Division Two U-19 Youth League, Zaria Centre, a filin wasa na Nasara Stadium, Zaria.

Wasan ya kasance mai cike da fafatawa da ƙoƙarin samun nasara daga kungiyoyin biyu.

🎥 Ga wasu daga cikin manyan abubuwan da s**a faru a wasan — HIGHLIGHTS!

⚽ Queens Planet FC 🆚 Flash Football
🏆 NLO Division Two U-19
📍 Nasara Stadium, Zaria

🚨Rahotanni daga wasu kafafen yaɗa labarai na Spainia sun bayyana cewa, a kwanakin nan, Real Betis na shirin fara zawarci...
20/08/2026

🚨Rahotanni daga wasu kafafen yaɗa labarai na Spainia sun bayyana cewa, a kwanakin nan, Real Betis na shirin fara zawarcin Karim Benzema, idan har ɗan wasan ya bar Al-Hilal a wannan bazarar.

Hakan na iya sawa dan wasan gaban ya sake fafata gasar La Liga a karo na biyu tun bayan da yabar kungiyar kwallon kafar Real Madrid.

NLO DIVISION TWO U-19 YOUTH LEAGUE📍 Filin Wasan Nasara Stadium, Zaria⏰ 11:00 na dare⚽ Croc City 🆚 Queens Planet FCKu shi...
20/08/2026

NLO DIVISION TWO U-19 YOUTH LEAGUE
📍 Filin Wasan Nasara Stadium, Zaria
⏰ 11:00 na dare
⚽ Croc City 🆚 Queens Planet FC

Ku shirya don kallon wani gagarumin wasan ƙwallon ƙafa na matasa, yayin da ƙungiyoyin biyu za su fafata domin samun maki uku a wannan Ranar Wasa ta 2! 🔥

🏆 Nigeria Premier Football League (NPFL)
🇳🇬 NLO Division Two U-19 Youth League
Wace ƙungiya za ta yi nasara? ⚽🔥

 # Abubuwa 6 da INEC ta haramta game da yaƙin neman zaɓeYayin da yaƙin neman zaɓe na babban zaɓen Najeriya na 2027 ya fa...
20/08/2026

# Abubuwa 6 da INEC ta haramta game da yaƙin neman zaɓe

Yayin da yaƙin neman zaɓe na babban zaɓen Najeriya na 2027 ya fara, jam’iyyun siyasa da ’yan takara sun samu damar bayyana manufofinsu da shirye-shiryensu ga masu zaɓe. INEC ta tanadi dokoki domin tabbatar da cewa yaƙin neman zaɓen ya gudana cikin lumana, mutunci da bin doka.

A ƙarƙashin **Electoral Act 2026**, akwai wasu abubuwa da aka haramta yayin yaƙin neman zaɓe.

# # # 1. Amfani da kalaman batanci da tayar da hankula

Ba a yarda jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da kalaman batanci, zagi, ɓatanci ko kalaman da za su iya tayar da hankalin jama’a ba.

Haka kuma, ba a yarda a yi amfani da kalaman da za su iya jawo ƙiyayya ko rikici tsakanin al’umma bisa addini, ƙabila, kabila ko wani ɓangare na al’umma ba.

# # # 2. Amfani da wuraren ibada da wasu wuraren gwamnati wajen yaƙin neman zaɓe

Dokar ta haramta amfani da **masallatai, coci-coci da sauran wuraren ibada**, tashoshin ’yan sanda da ofisoshin gwamnati wajen gudanar da gangamin siyasa ko tallatawa ko s**ar jam’iyya da ’yan takara.

# # # 3. Amfani da ’yan daba ko ƙungiyoyin tashin hankali

Jam’iyya, ɗan takara ko mai neman takara ba zai iya ɗaukar ma’aikata, horarwa ko shirya wasu mutane domin amfani da ƙarfi ko tilastawa wajen cimma wata manufa ta siyasa ba.

Wannan mataki na da muhimmanci musamman saboda tarihin tashe-tashen hankula da ake samu a wasu lokutan yaƙin neman zaɓe a Najeriya.

# # # 4. Barazana ko amfani da tashin hankali

Ba a yarda ɗan takara, jam’iyya ko magoya bayansu su yi wa wani mutum barazana da ƙarfi ko tashin hankali domin tilasta masa goyon bayan wata jam’iyya ko ɗan takara ba.

Wanda ya karya wannan doka zai iya fuskantar hukunci, ciki har da tara ko ɗaurin gidan yari, gwargwadon tanadin dokar.

# # # 5. Yin yaƙin neman zaɓe bisa addini ko ƙabila

Dokar ta haramta amfani da addini, ƙabila ko wata ma’anar bangaranci wajen yaƙin neman zaɓe domin tallata ko ƙin wani ɗan takara ko jam’iyya.

Wannan na nufin ’yan siyasa ya kamata su mayar da hankali kan **manufofi, shirye-shirye da abubuwan da za su amfani jama’a**, maimakon amfani da bambancin addini ko ƙabila wajen neman kuri’a.

# # # 6. Ci gaba da yaƙin neman zaɓe bayan wa’adin da doka ta kayyade

Dokar ta tanadi cewa yaƙin neman zaɓe na jama’a zai fara ne cikin wa’adin da doka ta kayyade, sannan ya ƙare **sa’o’i 24 kafin ranar zaɓe**.

Saboda haka, jam’iyyu da ’yan takara ba su da izinin ci gaba da tallata kansu ko gudanar da yaƙin neman zaɓe bayan lokacin da doka ta kayyade.

# # # Muhimmancin bin dokar

INEC ta jaddada cewa yaƙin neman zaɓe ya kamata ya kasance bisa manufofi, cikin lumana kuma a cikin tsarin doka. Hukumar na da alhakin sa ido kan harkokin yaƙin neman zaɓe da kuma samar da dokoki da za su jagoranci jam’iyyu da ’yan takara.

A babban zaɓen 2027, zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Tarayya an tsara gudanar da su ne a **20 ga Fabrairu 2027**, kamar yadda INEC ta bayyana a sanarwar farko ta jadawalin zaɓen.

**Manufar dokokin ita ce tabbatar da cewa siyasa ta kasance ta manufofi da gasa cikin adalci, ba ta zagi, ƙiyayya, tashin hankali ko tsoratar da masu zaɓe ba.**

Atiku Ya Yi Alkawarin Dawo Da Tallafin Man Fetur Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa 🇳🇬Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya ...
20/08/2026

Atiku Ya Yi Alkawarin Dawo Da Tallafin Man Fetur Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa 🇳🇬

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai tsaye da ya gudanar a shafinsa na Facebook, yayin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin cire tallafin man fetur ga rayuwar ’yan Najeriya.

Me kuke ganin wannan alkawari na Atiku zai iya haifarwa idan ya zama shugaban ƙasa?

🗣️ Ku bayyana ra’ayinku a cikin comments.

20/08/2026

AN ƘADDAMAR DA TITIN SHAGARI ROAD DA RIVER ROAD NA KWARU

Nuruddeen Muhammad Mujahid, SSA Strategic Communication to His Excellency Governor Uba Sani, yana daga cikin waɗanda s**a taka muhimmiyar rawa wajen shirya da gudanar da wannan taro.
Taskar Hausa JKD Media Alboom Hausa TV Senator Uba Sani

Address

Badarawa Main Road
Kaduna

Telephone

+2348164363661

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share