22/06/2026
Dalibai 630 Sun Kammala Shirin Koyon Sana’o’i na Abdulazeez Kaka Kashi na 11
A ranar Asabar 20/06/26 ne, dalibai 630 s**a kammala karatun koyon sana’o’i a karkashin Shirin Horas da Sana’o’i na Abdulazeez Abubakar Kaka (Abdulazeez Kaka Skills Acquisition Programme) na rukuni na 11, wanda ya kasance wani babban mataki na ci gaba wajen bunƙasa rayuwar matasa da al’umma baki ɗaya.
Tun bayan ƙaddamar da wannan shiri, fiye da mutum 5,000 sun amfana da horo da koyon sana’o’i daban-daban da s**a haɗa da fasahar zamani (Technology), harkokin kasuwanci (Entrepreneurship) da sana’o’in hannu, domin su samu dogaro da kai tare da ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.
Taron yaye daliban ya samu halartar Babban Baƙo na Musamman, Malam Aminu Zaria, Darakta Janar na Tinubu/Uba Sani Mobilization Network, tare da sarakunan gargajiya, shugabannin jam’iyya, jagororin al’umma da sauran masu fatan alheri.
Wannan shiri na tallafa wa manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma SUSTAIN Agenda na Gwamna Uba Sani, ta hanyar bai wa al’umma damarmakin koyon sana’o’i da dabarun dogaro da kai, ƙara yawan aiki, da samar da ingantacciyar rayuwa mai ɗorewa.
Shirin na ci gaba da gina matasa masu ƙwarewa, masu zaman kansu da kuma masu bayar da gudunmawa ga ci gaban al’ummominsu da ƙasa baki ɗaya.
Kowa Namu Ne ✌🏽♾️