19/02/2026
Farfado da Fannin Lafiya: Wasu daga cikin Muhimman Nasarorin Gwamna Abba K Yusuf
1. Mayar da Ma'aikata 926: Mayar da ma'aikata 926 kan tsarin albashin jiha tare da cikakken alawus na CONHESS, domin dawo da karsashi da tabbatar da adalci.
2. Daukar Sabbin Ma'aikata: Daukar kwararrun likitoci 250 da ma’aikatan lafiya (CHEWs), malaman jinya (nas-nas), da ungozomomi 155 domin magance karancin ma’aikata.
3. Tura Likitoci domin Samun Kwarewa: Tura likitoci 65 masu karatun kwarewa (Residency Doctors) domin inganta ingancin ayyukan asibitocin mataki na biyu.
4. Kara Karfin Ilimi: Gudanar da shirye-shiryen horarwa ga dukkan rukunonin ma'aikatan lafiya domin karfafa kwarewarsu ta aiki.
5. Samar da Tsaro a Asibitoci: Daukar ma’aikatan tsaro (security guards) 250 tare da horar da su domin samar da tsaro da tarbiya a muhallan asibitoci.
6. Shiga Gaba Wajan Samun Tantancewa: Samun amincewa (accreditation) ga shirye-shiryen karatun digiri na biyu a fannin haihuwa (O&G), likitancin cikin gida, kunne da hanci (ENT), da likitancin iyali.
7. Daukar Nauyin Karatu: Daukar nauyin likitoci don karatun kwarewa da digiri na biyu (Masters) a fannoni daban-daban na likitanci.
8. Tantance Sabbin Ma'aikata: Tantance sama da kwararrun ma'aikatan lafiya 2000 (Likitoci, Nas-nas, Pharmacists da sauransu) wadanda za a dauka aiki nan da ‘yan watanni.
9. Maido da Asusun Juya Kudin Magani (DRF): Farfado da asusun juya kudaden magani (Drug Revolving Fund) domin tabbatar da gaskiya da dorewar samar da magunguna.
10. Gyaran Asibitoci: Gyarawa da inganta manyan asibitoci (Secondary Health Facilities) sama da 20 a fadin jihar.
11. Samar da Hasken Solar: Sanyawa asibitoci hasken rana (solar) domin tabbatar da dorewar wutar lantarki don inganta kulawa da marasa lafiya.
12. Kayayyakin Zamani: Samar da na'urorin kiwon lafiya na zamani a asibitoci domin kaiwa matsayin duniya.
13. Samar da Kayayyakin Haihuwa Kyauta: Samar da kayayyakin haihuwa da na gaggawa (A&E) kyauta a kowane wata, inda aka ware guda 6,000 don haihuwa ta al'ada da 500 don fida (CS) domin rage mace-macen mata.
14. Samar da Cibiyar Abba Care: Gina cibiyar "Abba Care Center"—cibiyar bayar da magani kyauta ga masu cutar sikila (sickle cell), wadda ita ce irinta ta farko a yankin.
15. Kula da Lafiyar Yara Kyauta: Samar da ayyukan jinya da magunguna kyauta a Asibitin Yara na Hasiya Bayero da Asibitin Mata na Marmara.
16. Tabbatar da Tsaftar Asibitoci: Samar da kayayyakin tsafta a kowane wata ga dukkan asibitocin karkashin hukumar HMB domin dakile yaduwar cututtuka.
17. Samar da Kayayyakin Rubutu: Samar da kayayyakin rubutu na asibiti (stationery) na darajar N93 miliyan a kowace morar shekara (quarter) don tafiyar da ayyukan gudanarwa.
18. Inganta cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko (Primary Healthcare Centers) : Gyarawa da samar da kayan aiki ga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) sama da 200 a fadin kananan hukumomi 44.