Hanyar Kano

Hanyar Kano Domin sanin halin da hanyoyin Kano ke ciki, don kaucewa cunkoso, samun bayanai kan yanayin tsaro…

Wata mota ta k**a da wuta ta kone a gadar Kofar Ruwa dake kan t**i Katsina Road.📷Kano City
26/10/2026

Wata mota ta k**a da wuta ta kone a gadar Kofar Ruwa dake kan t**i Katsina Road.

📷Kano City

Hukumar Kasuwar Singa ta sanar da rufe hanyar Bello Road da ke cikin kasuwar da ke Kano, saboda fara aikin girka shingen...
26/10/2026

Hukumar Kasuwar Singa ta sanar da rufe hanyar Bello Road da ke cikin kasuwar da ke Kano, saboda fara aikin girka shingen kariya daga hadura.

A cewar Shugaban Gamayyar Kungiyar Ci Gaban Kasuwar Singa da Kewayenta (SIMDA), Alhaji Junaidu Muhammad Zakari, an fara aikin ne a yau Litinin da karfe 8 na safe, kuma zai lashe tsawon makonni biyu har zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba.

Kungiyar ta roki 'yan kasuwa, direbobi da sauran masu amfani da hanyar da su yi hakuri tare da bai wa masu aikin hadin kai domin kammala aikin cikin nasara. Haka kuma ta gargadi duk wanda ya yi yunkurin karya doka ta hanyar shigar da abin hawa cikin hanyar da aka rufe cewa zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Me yasa idan dare yayi mutane ke kin bin umarnin danger akan titunan Kano ?
25/10/2026

Me yasa idan dare yayi mutane ke kin bin umarnin danger akan titunan Kano ?

Titin kasuwar Farm Center kenan yayin da ake cigaba da aikin gyaran t**in na Farm Center.📷Aliyu Umar
25/10/2026

Titin kasuwar Farm Center kenan yayin da ake cigaba da aikin gyaran t**in na Farm Center.

📷Aliyu Umar

Gadar Sabon Gari.Kasuwanni nawa wannan gada ta hada ?📷Muhammad Khabir
24/10/2026

Gadar Sabon Gari.

Kasuwanni nawa wannan gada ta hada ?

📷Muhammad Khabir

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta mayar da wasu jami’anta biyu daga sashen hukumar dake...
24/10/2026

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta mayar da wasu jami’anta biyu daga sashen hukumar dake Kofar Nasarawa zuwa hedikwatar hukumar, bayan korafe-korafen da ake yi kansu na zargin karɓar cin hanci da kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.

Shugaban hukumar, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ne ya amince da matakin, wanda ya haɗa da cire jami’an biyu daga muk**an da suke riƙe da su, sauya wurin aikin, wadda Daraktan Gudanarwa da Ayyukan Gabaɗaya, Comrade Mahmud Haido, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an riga an aika wa jami’an wasiƙun neman bayani domin fara binciken zarge-zargen da ake yi musu.

KAROTA ta bayyana cewa tana ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da rashawa a cikin ayyukanta, tare da jaddada cewa za ta ɗauki matakan ladabtarwa bisa ƙa’idojin ma’aikatan gwamnati idan bincike ya tabbatar da laifi. Hukumar ta kuma gargaɗi jami’anta da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da riƙon amana, tana mai cewa an kafa ta ne domin yi wa al’umma hidima, ba don danniya ko karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.

Source: Lumana Radio

Cikin Hotuna: Yadda akan samu cunkoson ababen hawa a Gadar Hotoro a daren Juma’a, 23/10/2026. Hotunan sun nuna yadda jam...
23/10/2026

Cikin Hotuna: Yadda akan samu cunkoson ababen hawa a Gadar Hotoro a daren Juma’a, 23/10/2026.

Hotunan sun nuna yadda jama’a da ababen hawansu ke ta faman fata lokacin a kan t**in.

📷Labarai24

Gadar sama ta kofar Nasarawa kenan, Kanawa a zamanin wane Gwamna a kayi wannan gada ?📷Muhammad Khabir
23/10/2026

Gadar sama ta kofar Nasarawa kenan, Kanawa a zamanin wane Gwamna a kayi wannan gada ?

📷Muhammad Khabir

Sha tale-talen Club Road kenan.Kanawa ku fada mana asalin sunan Club Road a comment section?
23/10/2026

Sha tale-talen Club Road kenan.

Kanawa ku fada mana asalin sunan Club Road a comment section?

Address

Kano
700001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hanyar Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category