06/05/2026
SANATA RUFA’I HANGA: JAGORAN DA YA KAWO CANJIN FASALIN KANO CENTRAL!
Ba baki kawai ba, ayyuka ne suke magana! Cikin shekaru uku (3) kacal, Sanata Rufa’i Hanga ya tabbatar wa duniya cewa idan har akwai kishin talaka, to ana iya kawo canji koda ba kai ne Gwamna ba. Ga dalilan da s**a sa Sanata Hanga ya zama garkuwar talakan Kano Central:
1. TALLAFIN DOGARO DA KAI (Empowerment)
Domin kawar da zaman kashe wando da bunkasa tattalin arzikin karkara, Sanatan ya raba:
Ababen Hawa: Motocin Peugeot, Sharon, da wasu nau’ukan guda 52, tare da babura sama da 591 domin saukaka zirga-zirga.
Tallafin Sana'a ga Mata: Mata sama da 1,000 sun sami jarin N20,000 zuwa N50,000. Ya raba kekunan dinki 744, injinan markade 300, da injinan taliya 2,115.
Sana’ar Maza da Matasa: Ya horar da matasa 100 aikin aski (tare da basu kayan aiki da hasken Solar), 200 aikin kera takalmi, da 100 aikin gyaran Solar.
Harkar Noma da Kiwo: An raba takin zamani ga manoma 3,000, injinan ban-ruwa 2,000, mini-tractors 31, da tallafin kiwon kifi da kaji ga mutane sama da 1,000.
2. ILIMI DA FASAHAR ZAMANI (Education & Tech)
Ilimi shine hasken rayuwa, kuma Sanata Hanga ya ba shi kariya:
Fasahar AI: Ta hanyar gidauniyarsa, yana koya wa marayu 30 fasahar AI da tsara yanar gizo tare da basu N5,000 na mota kowane mako.
Gina Makarantu: Ya gina azuzuwa da bandakuna a wurare 41, ya gyara makarantun boko da na addini 87, sannan ya gina sabbin Islamiyyoyi 21.
Tallafin Karatu: Ya raba takardar Jamb ga dalibai 1,115, ya ba wa daliban BUK 200 tallafin karatu, sannan wasu sama da 1,000 a makarantun gaba da sakandare daban-daban.
3. AYUKAN CIGABA (Capital Projects)
Sanatan ya maida Kano Central tamkar gidan gona:
Tituna: An gina tituna a Dawakin Kudu, Warawa, Garin Mallam, Kumbotso (3), Nasarawa (4), Fagge, Dala, Municipal, da Tarauni.
Ruwan Sha: An gyara tsoffin famfunan tuka-tuka (boreholes) 315, aka kuma gina sabbi 17.
Wutar Lantarki: Ya samar da Mini Solar Grid a wurare daban-daban da kuma raba manyan Transformers don haskaka gari.
4. JINKAI DA TAIMAkon AL’UMMA
Binne Mamata: Ya samar da tukwane 500,000 da likkafani 500,000 don saukaka wa iyali radadin mutuwa.
Aikin Yi: Ya samar wa matasa aiki na d